Manyan labarai daga jaridun Najeriya

Manyan labarai daga jaridun Najeriya

Manyan labarai daga jaridun najeriya a yau Laraba 20 ga watan Yuli

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa mutane uku daga cikin wadanda ke fuskantar shari’a kan zargin cin hanci da rashawa, suna dokin mayar da” kudaden da suka sata” domin samun yanci. Mutane ukun sun hada da Olisa Metuh, Adeshola Amosu, da Mohammed Dikko Umar.

Manyan labarai daga jaridun Najeriya

Jaridar Daily Sun ta ruwaito inda Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci yan Najeriya da suyi watsi da yunkurin da wasu marasa kan gado keyi na ganin sun shafa kashin kaza ga martaban ministoci da kuma wasu mayan jami’an gwamnati, kan zargin aikata cin hanci da rashawa ba tare da kwakwarar hujja ba.

A cikin jaridar Vanguard mun samu rahoto kan cewa, babban bankin kasa wato Central Bank of Nigeria (CBN) tayi Magana game da halin da tattalin arziki ke ciki. Inda take cewa, yawan ci gaba da kai hare-haren bam a yankin Niger Delta ya taka muhimmin rawa gurin dakushe tattalin arzikin kasar najeriya.

A jaridar The Guardian kuma, munji cewa, mataimakin shugaban majalisar dattawa ta kasa, Ike Ekweremadu ya bi layin masu goyon bayan sabonta fasalin al’amuran Najeriya.  A cewar sa sake fasalin ne kawai zai kawo karshen matsalolin da kasar ke fuskanta a yanzu.

A karshe jaridar Punch ta ruwaito cewa, abin bakin ciki ya faru a ranar Talata, 19 ga watan Yuli, a karamar hukumar Ipaja, dake jihar Lagas, sakamakon wasu yan’uwa biyu suka mutu a gobara, wanda ake zargin wutar kendir ya haddasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel