Zan shugabanci soji da kaina mu damke Akwaza - Ortom

Zan shugabanci soji da kaina mu damke Akwaza - Ortom

–Gwamnan Jihar Benuwe ya dau alwashin damke akwaza wanda ke da hannu a cikin kisan ma'aikacin sa, Denen Agbana.

–Ortom ya siffanta akwaza a matsayin alade wanda ya sanya cikin gwamnatin shi ,amma yana zama annoba ga gwamnatin.

–Ortom ya dau alwashin tabbatar da tsaro a Jihar Benuwe

Gwamna Samuel Ortom ya dau alwashin shugabantan jami'an tsaro domin damke Terwase Akwaza,wanda aka sani da gana, ta dalilin kisan gilan da akayi ma Denen Igbana. Gana ,wanda ke da hannu dumu-dumu a cikin kisan mai tsaron Ortom, igbana, ya arce daga ganin jama'a. Amma game da Ortom, zai shugabanci Soji da sauran  jami'an tsaro da kansa domin binciko inda gana yake da kuma dakke shi.

Gwamnan Jihar ya fadi hakan je a ranar litinin ,18 ga watan yuli yayinda yan kungiyar Cigaban Ugondo suka ziyarce shi a gidan gwamnati, gwamna ortom ya siffanta gana a matsayin alade wanda aka baiwa aikin yaki da aikata laifuka amma yana yana zama kaya mai sukar gwamnatin sa a ido.  Jaridar the Nation ta bada rahoto.

Zan shugabanci soji da kaina mu damke Akwaza - Ortom
gwamna samuel ortom

Ya ce: " Nayi nufi mai kyau amma ban san angulu zata koma gidanta na ysamiya ba. Zan saba masa ,shi da yaransa;, zan shugabanci jami'an tsaro domin kamashi

Gwamnan yayi alkawarin goyon baya da karfafa yan banga domin yaki da aikita laifuffuka. Ya kara da cewa Hukumomin tabbatar da bin dokokin kasa na bukatan kusanci da juna ko wasu kungiyoyi domin cin nasara. Yace gwamnatinsa zata bada kayan aiki domin tabbatar da tsaro kuma yana baiwa yan banga shawaran to dau aniya mai kyau. Bayan haka ,ya umurci mai basa shawara akan harkokin tsaro da ya hada kan kungiyoyin yan banga zuwa bai daya kacal saboda sawwaka isar taimakon gwamnati wurinsu.

KU KARANTA : Tashin hankali: Fulani Makiyaya sun kai farmaki Jihar Abiya

Jaridar NAIJ. Com ta tuna cewa kisan Igbana ta sa sun dukufa cikin addua da azumi domin rokon Ubangiji akan Jihar Benuwe, a hakan ne GWAMNA ortom ya shinfide a kasa yayi kuka domin neman taimakon Allah. Ortom yayi kira ga mabiya addinin kirista da su dukufa cikin rokon Ubangiji ya kunyata duk wanda ke son ganin bayan wannan gwamnatin.

An kashe Denen Igbana ne yayinda yan bindiga suka far ma gidansa a ranar juma'a, 20 ga watan mayu misalin karfe 2:30 na safe. Game da gwamnan, kisan igbana babban rashi ne ga gwamnatin sa, ya yi alkawarin sai gano Wadanda suka aikata ta'asan.

 

 

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: