Jihar Ribas na tuhumar Amaechi da handaman kudin jama’a.
– Ana tuhumar rotimi Amaechi da wawure kudin mutanen jihar Ribas
– Kwamishanan yada labarai yace amaechi ya amsa bashi daga babban bankin tarayya domin amfanin kansa
– Jam'yyar APC ta musanta zargin kuma ta sifanta shi a matsayin bogi.
Gwamnatin Jihar Ribas ta sanar da wata babban zargi akan tsohon gwamnan jihar, chibuike rotimi amaechi,cewa ya handame kudi N3tirilyan yayinda yake gwamna. Amaechi yayi gwamnan Jihar Ribas tsakanin shekarar 2007 da 2015 kafin shugaba Muhammadu Buhari ya nada shi a matsayin ministan tafiye-tafiye
Jaridar Daily Trust ta bada rahoton cewa Dakta Tam- George wanda shine kwamishanan yada labarai na Jihar yace Amaechi ne ya bar ayyuka da ba'a gama ba mafi yawa a tarihin Jihar. Kwamishanan ya cigaba da cewa gwamnatin amaechi ta amsa bashin kudi N4bn na aikin noma daga babban bankin tarayya kuma babu wani shaidar manomin da ya amfana . Yace gwamna Nyesom Wike ya amsa bashin N2 biliyan daga babban bankin tarayya kuma an samu manoman da suka amfana 35,000 manya da yaran ‘yan kasuwa.
KU KARANTA : Kotun Abuja tayi watsi da neman belin Omisore.
Jam'yyar APC kuwa,tace bazai yiwu tsohon Gwamnan ya yi watsi da kudin jama'a haka ba. Kakakin jam'yyar APC na Jihar Ribas, Mr. Chris Finebone, yayi watsi da zargin kuma ya tuhumi kwamishanan yada labarun da kara wa aya zaki. Finebone yace: “Sau daya ,ku tambayi kwamishanan cewa dame akayi ayyukan da yace ba'a kammala ba. Ya nada muhimmanci ya duba tarihin shi saboda ya farka daga mafarkin shi.”
Amma, Soji Adagunodo, shugaban jam'yyar PDP ta Jihar Osun yace nufin yaki da rashawan da Shugaba Buhari ke yi kawai domin danne yan adawa ne.
Game da Jaridar The Punch, shugaban jam'iyyar PDP na Jihar osun din yace yaki da rashawan bangaranci ne.
Asali: Legit.ng