Uwa da ‘ya sunyi dambe akan saurayi

Uwa da ‘ya sunyi dambe akan saurayi

Wani abin kallo tamkar wasan kwaikwayo ya faru yayinda wata mata bazawara mai yara 4 tayi dambe da yarinyarta da ta Haifa a kan saurayi a Nyanya,Abuja.

Uwa da ‘ya sunyi dambe akan saurayi

Rahotanni sun nuna cewa matan guda 2,uwa da ‘ya sun baiwa hammata iska saboda saurayi a gaban jama’a. matan yar kudancin Najeriya ce ,ta na sayar da giya da barasa ne a unguwar,kuma yarinyarta dalibar jami’ar Jihar Nasarawa,duk da dai ba wanda ke da tabbacin yar makaranta ce da gaske. Wata majiya ta fada ma Pulse.ng

“Abin ban mamaki ne da aka mace yar kimanin shekaru 40 da kari ,ke dambe da hahuwar cikinta yar shekaru 22 a gidan giya. Sunyi dambe ne sosai, har suka tara ma ansu jama’a. sun keta kayan juna har ya kai kayan ciki ya rage a jikinsu. Daga baya muka gano dalilin fadan, ashe wani namiji ne ke soyayya da uwa da ‘ya yana faskanci da su.

KU KARANTA : Me musulunci yace game da zaman aure da ‘ya mace?

“Daga baya da aka samu sasanta su, muka tambayesu shin menene dalilin damben, uwar ta yi shiru har sai da yarinyar tace mahaifiyarta ta kwace mata saurayinta da ke kula da ita,yana daukan nauyin karatun ta. Ita uwar sai ta fara Magana, tace abin da ya faru shine, ta shekara biyar tana soyayya da mutumin kafin ‘yarta ta mata kwace. Tace bai wuce shekara daya da mutumin ya fara kwanciya da ‘yar ba. Wannan wani irin abin kunya ne?.

Asali: Legit.ng

Online view pixel