Tsinuwa ta biyo bayan yin hoton ‘Dab’ a Makka

Tsinuwa ta biyo bayan yin hoton ‘Dab’ a Makka

Wasu mata ‘yan Najeriya sun shiga bakin duniya da Allah wadai sakamakon wa rawar ‘dab’ da suka yi a kasa mai tsarki

-An danganta rawar ga masu bautar shaidan wacce ta samu asali ga hadiman firauna

- Daukar hoton dab ya zama yayi

Tsinuwa ta biyo bayan yin hoton ‘Dab’ a Makka

A kokarin su na tafiya da zamani wasu mata ‘yan Najeria sun sha luguden Allah wadai da tir sakamakon yin hoton dab a Makka.

Hoton matan sanye da hijabi da zanen atamfa rahotanni na cewa sun je kasa mai tsarki ne aikin ummara amma suka bige da yin hoton ‘dab’ wacce ake ganin bai dace ba.

KU KARANTA: Fursuna ya tsere daga kurkuku a tsirara

A binciken da Aliyu Umar Musa wani mai lura da al’amuran yau da kullum ya sa a shafin sada zumunta da muhawara na whatsapp ya ce “rawar sabon salon bautar Iblis ce daga kungiya illuminati, sannan ya kara da cewa    

“Ma'anar Dab dai shine, rufe fuska da hannun hagu ko dama sai hannu dayan a mikar da shi. Masu shan tabar Iblis wato wiwi sun kasance suna amfani da wannan kalma ne a lokacin da suka zuki tabar wiwi din da suke sha. Ma'ana idan ka zuki tabar ta wiwi sai ka noke fuskarka a cikin hannunka daya shi kuma dayan ka rike tabar ta wiwi da shi.

Tsinuwa ta biyo bayan yin hoton ‘Dab’ a Makka

Rawar ta samo asali ne daga wani mawaki da ake kira da Migos wanda shi ne mawakin da ya fara yin wannan rawar tare da yi mata waka, sannan sai dan wasan kwallon zari ruga Cam Newton ya watsa wannan rawa a duk lokacin da ya ci wasan sa, sai kuma wani mawaki mai suna "Jay-Z" (wanda kowa ya san cewa shi ne shugaban masu bautar Shaidan) ya yi wannan rawa a cikin wata wakarsa mai suna “Fuck With Me You Know I Got It”. Daga nan Sai sauran mawaka da 'yan Kwallon kafa suka dauki wannan dab dance din suka juyar da shi a zuwa dab Picture.

Shin ko menene ra'ayinku dangane da wannan?

 

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng