Kasar Amuruka ta fayyace zargin da ake ma Matar shugaba Buhari
Gwamnatin kasar Amuruka ta fitar da wata sanarwa dauke da martani zuwa ga Gwamnan jihar Ekiti watau Ayodele Fayose a inda suka tsarkake uwar gidan shugaba Buhari daga zargin da yayi mata na cewa tana da laifi a kasar
Haka zalika kasar ta Amuruka ta ce bata neman uwar gidan Aisha Buhari kamar dai yadda gwamnan ya yi ikirari. Shidai gwamnan na Ekiti a ranar wata Litinin 20 ga watan da ya gabata ya rarrabawa manema labarai wani kundin wanda ya ke dauke da sunan Aisha Buhari a cikin jerin masu laifin satar kudi.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa jami'in hulda da jama'a na offishin jakadancin kasar Amuruka a Najeriya Frank Sellin shine ya aika da sakon emel dauke da hakan zuwa ga manema labarai inda ya a ciki ya bayyana hakan. Sellin din ya aike da sakon emel din ne a matsayin amsa ga wani dan jaridar da yayi masa tambaya game da gaskiyar zancen na zargin da Fayose yayi ma Aisha Buhari.
Sellin sai yace: "Bamu da wani bayani game da hakan." A kwanan bayan dai Fayose ya fitar da wani zancen da ya girgiza kowa inda ya ce Aisha Buhari na da laifi a kasar Amuruka kuma ma suna nemanta ruwa a jallo tare kuma da cewa shima Buharin ba wani tsarkakkake ne ba.
Fayosen ya cigaba da cewa: "ai ita ma uwar gidan shugaba Buhari din tana da hannu a cikin badakalar Halliburton. Sadda Kasar Amurukan ta kama Jefferson, ai ya bayyana cewa Aisha Buhari na da hannu a ciki." "Kuna ma iya dubawa akwai sunan ta a cikin feji na 25."
Asali: Legit.ng