Kungiyar PSG na neman dan wani wasan Atletico Madrid

Kungiyar PSG na neman dan wani wasan Atletico Madrid

Kungiyar PSG na neman dan wasan Atletico Madrid.

– Griezmann ya sanya hannu a wani sabon kwantiragi da Athletico Madrid.

– Wani Darektan Atletico Madrid ya tabbatar da cewa suna tattaunawa da Kungiyar PSG.

– Dan wasan na Kasar Faransa zai yi zaman sa a Atletico har Shekarar 2021.

Wani darektan Atletico Madrid Eric Olhats ya tabbatar da cewa Kungiyar PSG na neman dan wasan gaba A. Griezmann. Dan wasan dai bai dade da sanya hannu a wani sabon kwantiragi na shekaru 5 ba da kungiyar da Atletico Madrid. Kungiyoyi da dama ne dai ke neman dan wasa A. Griezmann bayan da ci ma Atletico Madrid kwallaye 32 a gasar wasannin wannan shekara.

A SAUKE MANHAJAR MU NA Legit.ng DOMIN SAMUN LABARIN WASANNI.

Darektan wasannin Kungiyar Atletico Madrid Olhats ya tabbatar da wannan labari. Yace yanzu haka ana tattaunawa da kungiyar PSG, domin suna neman dan wasan. Olhats yana mai cewa: “Muna tattaunawa da Kungiyar PSG (Ta darektan wasanni su, mai suna Olivier Letang). PSG na neman dan wasan mu, muna kuma sauraron su, kungiyar PSG babban kulob ne… Muna kokarin ganin dan wasan mu ya zauna, haka kuma, muna duba halin da ke kasa, sai dai sanin gobe sai Allah.” Olhats ya kara da cewa: “Zai yi kyau Griezmann ya koma inda zai ci kofuna, sai dai Kungiyoyi irin su Barcelona da Real Madrid ba su neman wani dan wasan sama (mai cin kwallaye) a yanzu haka.”

Kungiyar PSG na neman dan wani wasan Atletico Madrid

 

 

 

 

 

Dan wasa Antoine Griezmann dai ya taka rawar gani a gasar zakarun Nahiyar Turai na EURO da aka kammala wannan shekarar a kasar sa ta Faransa. Griezmann dai ya zuba kwallaye har 6 cikin wasanni 7 da ya buga. Griezmann dai ya rattaba hannu kan wani sabon kwantiragi da zai say a zauna a Atletico Madrid har nan da shekarar 2021.

KU KARANTA: BARCELONA TA SAYE SABON DAN KWALLO

 

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel