Arsenal na neman dan wasan Barcelona, Arda Turan

Arsenal na neman dan wasan Barcelona, Arda Turan

Labarin Sayayyen Kungiyar Arsenal

Arsenal na neman dan wasan Barcelona, ana kuma neman Sanchez, ina aka kwana a maganar tashin Wenger.

– Arsene Wenger na neman dan wasan Barcelona.

– Arsenal sun ce Alexis Sanchez ba na sayarwa bane.

– Wenger zai yi zaman sa a Arsenal.

Ga manyan labaran Sayayyen kakar bana na Kungiyar Arsenal.

Jaridar Marca ta kasar Spain ta rahoto cewa Barcelona na shirin saida tsohon dan wasan Athletico Madrid Arda Turan. Dan wasan na tsakiya mai shekaru 29 na iya komawa Arsenal a kan kudi fam milyan £23.

Arsenal na neman dan wasan Barcelona, Arda Turan

 

 

Sky Italia kuma ta rahoto cewa Arseanl na sa ran sayo dan wasan bayan Inter Milan akan kudi £15 miliyan. Arsenal dai na neman Jeison Murillo na kulob din Italiyar. Haka kuma Kungiyar Arsenal din na neman Mauro Icardi wanda ke kasuwa a halin yanzu, Matar dan wasan take cewa, abin ta ke iya fahimta shine, Icardi yana kasuwa, kuma kungiyoyin wasa da daba na kokarin sayen sa. Tana cewa, za su duba yanayin, domin Inter Milan din na cikin wani mawuyacin hali.

A SAUKE MANHAJAR MU NA Legit.ng DOMIN SAMUN LABARAI KAI TSAYE.

Kungiyar Juventus na Italiya ta tabbatar da cewa Arsenal sun yi watsi da yunkurin sayen dan wasan ta Alexis Sanchez da tayi. Juventus dai ta bada miliyan har fam £34 domin a saida mata dan wasan gaba na Kasar Chile Sanchez, sai dai Arsenal din ba su amince ba. Darektan Kulob din na Juventus Giuseppe Moratta ya bayyana haka, yana mai yaba ma dan wasan. Moratta yace Arsenal sun sanar da su cewa ba za su saida Sanchez din ba.

Rahotanni na nuna cewa Kasar Ingila na neman Arsene Wenger ya maye gurbin Roy Hodgson. Hodgson ya bar aikin ne bayan an kora Kasar Ingilar daga Gasar EURO na Turai. Wenger yace yana iya karbar aikin horar da Kasar Ingilar, ya bayyana Ingila a matsayin Kasar sa ta biyu. Amma yace yanzu haka, hankalin san a kan Arsenal.

KU KARANTA: DAN WASAN CHELSEA ZAI TASHI

Asali: Legit.ng

Online view pixel