Mace mai satar mutane ta tona asiri mai rikitarwa
-An kama wata mata yayin da take yunkurin sace wani yaro a jihar Lagas, a jiya Litinin 11 ga watan Yuli
-Mai satar mutanen ta bayyana cewa tana daga cikin kungiyar mata 27 da suke satan mutane a Jumhuriyyar Benin
-Mazauna garin sun bayyana cewa satar mutane ya yawaita a watan da ya wuce
Wata mata da haukan karya ta sace wani yaro, an kama ta a hanyar Aka, Okokomaiko na jihar Lagas, a ranar Litinin 11 ga watan Yuli
Mai satar yaran ta so ta tsere a cikin tawagar da suka zagaye ta amma an kama ta daga baya. Abu daya da ya ceceta shine bayyana gaskiya da tayi.
KU KARANTA KUMA: Fulani makiyaya sun kai hari jihar Niger, sun kashe mutane 11
A cewar ta, tana da wanda zai siya yaron da take shirin sacewa a kasa, ta kuma ce ba ita kadai bace take aikata hakan.
“Mu 27 ne muka zo daga jumhuriyyar Benin. An ba ko waccenmu wayar salula guda biyar domin kiran wadanda zasu siya mutanen da muka sato, musamman kananan yara. Sai mu bata wayar bayan mun gama ciniki don gudun a gano mu. Muna siyar da duk wanda muka sace ne, ba wai sai mun tara su ba.
Mazauna gurin sun ce suna ganin ta a unguwan tana abu kamar mai tabin hankali, amma an kama ta jiya tana yunkurin sace wani yaro.
Bisa ga abunda mazauna gurin suka bayyana wa jaridar Vanguard, an rasa kimanin yara bakwai a Okokomaiko, cikin watanni biyu da suka wuce.
An rahoto cewa a kwanakin baya da suka wuce a Okokomaiko, an kama wata mai satar yara, tayi nasarar sace wani yaro da farko, a yunkurinta na sace na biyun ne aka kama ta.
Asali: Legit.ng