Sakamakon Wasannin Gasar Premier League (Najeriya) Na Wannan Mako
Kungiyar Ikorodu United na cikin tsaka-mai-wuya a Gasar Premier League na Najeriya.
– Har yau Kungiyar Ikorodu United ba ta ci wasanta a gida ba.
– Shooting Stars na Garin Ibadan sun taso daga baya sun buge Nasarawa United da ci 2-1.
– Wikki Tourists sun dawo saman teburi bayan sun buga kunnen doki a gidan Warri Wolves
Ga dai cikakken sakamakon wasannin da aka buga a gasar Premier league na Najeriya a nan Kasa:
Kano Pillars 3-0 Lobi Stars
Kano Pillars ta doke Lobi Stars a filin wasa na Sani Abacha dake Kofar Mata a ranar Lahadin nan da ci uku da nema. Adamu Mohammed, Rabiu Ali da Jamiu Alimi ne suka ci ma Sai Masu Gidan kwallayen.
A sauke Manhajar mu domin samun labaran wasanni.
Shooting Stars 2-1 Nasarawa United
Nasarawa United ta fara cin Shooting Stars a minti na 18, sai dai Shooting Stars din sun taso daga baya sun zura ma Kungiyar Nasarawa United din ci biyu. Wannan ya sa tayi nasara gaban magoya bayan ta a Garin Ibadan da ci 2-1.
Plateau United 1-1 Akwa United
Plateau United sub buga 1-1 da Kungiyar Akwa United a Garin Jos. John Kelechi da Friday Ubong suka ci ma Kungiyoyin kwallaye a mintuna na 49 da 74.
Rivers United 1-0 Niger Tornadoes
Rivers United ta buge Niger Tornadoes da ci daya mai ban haushi. Bernand Ovoke ne ya ci ma Rivers United din kwallo a minti na 22 a wasan.
A sauke Manhajar mu domin samun labaran wasanni.
Ikorodu United 1-1 FC Ifeanyi Ubah
Ikorodu United ta buga kunnen doki da Ifeanyi Ubah a garin Legas. Sai dai wani ikon Allah ne zai hana Kungiyar Ikorodu United din yin kasa daga Gasar ta Premier League.
Warri Wolves 1-1 Wikki Tourists
Haka Warri Wolves tayi cangaras da Wikki Tourists a gidan na Wikki. Idris Guda ya ci ma Wikki Tourist sai dai daf a tashi Achibi E. ya ramo a Warri wolves. Yanzu haka, Wikki Tourist na saman teburin gasar, tare da Enugu Rangers.
El kanemi Warriors 3-1 MFM
El Kanemi Warriors na Maiduguri sun yi fata fata da MFM da ci 3-1 a ranar Asabar.
Enyimba 0-1 Heartland
Heartland sun ci zakarun gasar, Enyimba ci daya tal, mai ban haushi a wannan mako.
KU KARANTA: AN YI MA IYALAN MARAFA TAAZIYA
Asali: Legit.ng