Tirkashi : Fasto mai auren jinsi ya fito yayi magana

Tirkashi : Fasto mai auren jinsi ya fito yayi magana

Wani fasto dan Najeriya mai auren jinsi kuma wanda ya kafa cocin House of Rainbow Church mai suna ,macauley emmmanuel, dake zaune a kasar Ingila,yace Ubangijinsu ya basu auren jinsi ne saboda yana son su.

Faston ya fada ta kafar sadarwar sa ta Facebook abinda yayi ma yan uwansa da suka gujeshi ta dalilin zaban auren jinsi. Ku saurare shi:

“Sai da na daina taimaka ma dangi ,na fara taimaka wasu. Gaskiya ba dadi dangi su guji mutum musamman iyaye da yara,tunda na zama mai auren jinsi daya, wani zubin sai inyi tunanin kashe kaina saboda kiyayyan da ake nuna mini, amman Ubangiji na kiyaye ni.

“Ko da kadan ban damu ba saboda cocin mu House of Rainbow ta hada ni da mutane irina masu auren jinsi da dama,masu son yan jinsin dubbau.bgaba daya haka kuma,na samu kwanciyar hankali . ina fada ma mutane irina cewa Ubangijin mu na son mu kuma muna gode masa da hakan.

Tirkashi : Fasto mai auren jinsi ya fito yayi magana
fastin mai auren jinsin

 “ Auren jinsi daya na nufin ubangijin ka na sonka,ya yarda da kai. Littafin Jeremiah 1:5  da psalm 139:14 sun yi fadakar wa. Babu wani abin kunya dan ni mai auren jinsi ne,bani nadama koda kwayan zarra. Nayi aure shekarar 1991, da ikon ubangiji muka rabu 1994. Akwai mutane da dama da suke da abin fada amma ba'a sauraronsu. Kuyi hakuri idan na bata muku rai, kawai na fadi ra'ayi na ne. Nagode.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng