Dalilin da yasa na koma Leicester City Inji Ahmed Musa
Shahararren dan kwallon Najeriya kuma dan arewacin kasar Ahmed Musa ya bayyana dalilin da yasa ya zabi komawa kungiyar kwallon kafa ta kasar Ingila wadda kuma ta lashe kofin gasar a kakar wasan da ta gabata watau Leicester City.
Mataimakin jagoran tawagar kwallon kafar kasar Najeriyar dai Ahamed Musa ya rattafa wa wata yarjejeniyar shekaru 4 da kulob din Leicester City din. Hakan ne kuma ya maida shi ya zama na 4 a jerin cinikayyar da kungiyar tayi wannan kasuwar cinikayyar tun bayan da suka sawo Nampalys Mendy, Ron-Robert Zieler da kuma Luis Hernandez.
Dan kwallon a wata tattaunawa da yayi da gidan talabijin din kulob din ya bayyana dalilin sa na zabar kungiyar duk kuwa da cewa kungiyoyi da dama irin su Southampton, Everton da ma West ham duk sun nuna sha'awar su gare shi.
Ahmad Musa ya bayyana dalilin nasa ne da cewa kungiyar na daya daga cikin manyan kungiyoyin wasannin kasar kuma suna da karamci sosai. A cewar sa: "Nayi matukar farin ciki da na dawo nan kulob din kuma yanzu haka ina cike da jin dadi. A ganina kulob ne wanda ya shahara sosai kuma sun dauke ni kamar dan uwa. Na ji dadin yadda suke karramani."
"Yanzu haka dai na zaku ne sosai domin in gana da magoya bayan kulob din da kuma ganin yadda za'a fara kakar wasa mai zuwa." Ahmad Musa dai ya zura kwallaye 54 ne a cikin wasanni 168 da ya buga ma tsohon kulob din sa na kasar Rasha a cikin shekaru 5. Anan gida Najeriya kuma ya zura kwallaye 11 ne a cikin wasanni 58 da ya bugama kasar.
A kwanan baya ma dai shine jagoran kungiyar a nan gida Najeriya kafin daga bisani ya bada jagorancin don kashin kansa ga dan wasan tsakiya na Chelsea, John Obi Mikel.
Asali: Legit.ng