Shugaban hukumar fursuna ya yi karyar shekarun aiki

Shugaban hukumar fursuna ya yi karyar shekarun aiki

Ana zargin sabon shugaban hukumar fursunonin Najeriya watau Nigerian Prisons Service (NPS) Ja'afaru Ahmed da shirga karyar shekarun sa inji gidan jaridar nan na Sahara Reporters.

Shugaban hukumar fursuna ya yi karyar shekarun aiki
(NPS)

Wasu takardu dai da gidan jaridar na Sahara Reporters suka samu sun nuna cewa shugaban ya shiga aikin na fursuna ne a 30 ga watan Nuwambar 1985 lokacin yana da shekaru 28 kuma ranar haihuwar sa tana 21 ga watan Juli 1957.

Sahara Reporters din suka cigaba da cewa daga shekarar da ta gabata ne ta 2015 sai shekarun na haihuwar nasa suka canza inda ta koma 21 ga watan Juli 1959 wanda hakan ke nuna cewa shugaban ya samu karin shekaru biyu kenan na aiki.

Har ilayau dai jaridar ta Sahara Reporters ta ce wannan karin na shekarun da akayi anyi shi ne tare da sa hannun ministan cikin gida kuma na hannun damar shugaba Buhari General Abdulrahman Bello Dambazzau (rtd). Mai karatu zai iya tuna cewa shugaba Buhari ya amince da nadin shugaban na hukumar fursuna Ja'afaru Ahmed a matsayin wanda ya gaji Dr. Peter Ekpendu a 24 na watan Mayu, 2016.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng