Jana’izar Umaru Shinkafi a Sokoto (Hotuna)
-Marigayin shi ne marafan Sokoto
-Ya taba tsayawa takarar shugabancin kasar nan a
-Gwamnan Jihar Kebbi surkin marigayi ne
Ranar Laraba 6 ga watan Yuli ne aka yi jana’izar Umaru Shinkafi, marigayin wanda ya rasu a wani asibiti Landan, ya sha fama da rashin lafiya kafin rasuwar ta sa.
Gawar marigayin ta iso filin jirgin saman Sokoto ne a daga Landan, a gwamnan jihar sokoto Aminu Tabuwal da na jihar Kebbi Bagudu da kuma na Zamfara Abdulazeez Yari da kuma wasu daga cikin gwamnonin arewacin kasar suka tarbe ta, kafi a yi jana’izarsa a masallacin Sultan Bello da ke Sokoto.
Matar gwamnan jihar Kebbi kuma ‘yar marigayin Hajiya Zainab na daya daga cikin wandanda suka tarbi gawar a filin jirgin saman .
Alhaji Umaru Shinkafi shi ne Marfan Sokoto, ya taba zama shugaban jami’an tsaro na farin kaya NSA a shekarun 1984, ya kuma yin takarar shugabancin kasarnan a karkashin jam’iyyra ANPP. Ya kuma rasu ne a asibitin Harefield da ke titin end road a Middlesex a Britania.
Cikin ‘ya ‘yan marigayin da akwai Hajiya Zainab matar gwamnan Kebbi da kuma Hajiya Hadiza matar gwamnan jihar Zamfara Abdulazeez yari.
Asali: Legit.ng