Ummaru Shinkafi ya rasu
- Allah yayi ma ummaru Shinkafi rasuwa
- Ya rasu ne a jiya bayan yayi fama da rashin lafiya
- Ya rasu ne a kasar Ingila.
Allah yayi ma Ummaru Shinkafi rasuwa a jiya. Ya rasu ne bayan yayi fama da matsananciyar rashin lafiya a kasar Ingila.
Ummar Shinkafi kafin rasuwar shi yayi aiki tare da yan sanda sirri na Najeriya daga 1979 zuwa 1983. Sannan kuma yayi ma Olu Falae mataimakin shugaban kasa a takarar zabe ta 199. Asalin shi dai dan Zamfara ne kuma kuma yana rike ta Sarautar Marafan Sakkwato.
Jaridar Premium Times ta bayyana cewa za'a dawo da gawar shi a ranar Juma'a inda za'a binne shi a Makabartar Abubakar na Ukku dake a Sakkwato.
Ya rasu ya bar mata Daya da Ya'ya 5. A cikin su akwai Zainab Baugud, wadda ita ce matar Gwamnan Jihar Kebbi, da kuma Aisha wadda itace matar Gwamnan Jihar Zamfara.
Asali: Legit.ng