Abubuwan ban mamaki game Kasar Iceland da ba ka sani ba

Abubuwan ban mamaki game Kasar Iceland da ba ka sani ba

– Kasar Iceland ta zama mafi karantar Kasa da ta taba buga Gasar EURO

– Yawan Mutanen Kasar bai kai na wani jinsin dabbobin ba

– Kasar Iceland dai ta ba Ingila kashi a Gasar EURO 2016

Abubuwan ban mamaki game Kasar Iceland da ba ka sani ba
Euro 2016: Italy vs Germany

Kasar Iceland ce ta cire Kasar Ingila daga gasar kwallon kafar zakarun Nahiyar Turai, watau EURO 2016 da ake bugawa a wannan shekarar a Kasar Faransa. Sai dai Kasar Faransar tayi waje da Kasar Iceland din da ci har 5-2.

Ga wasu abubuwa na ban mamaki game da Kasar Iceland din:

 

- Wani abin ban mamaki kuma shine, Duwatsu masu-aman-wuta (Wanda ake kira Volacano) sun fi ‘Yan Kwallon Kasar yawa. ‘Yan kwallon kafar kasar basu wuce 23,000 (Amma sai dai 120 ne kacal wanda duniya ta san da su), yayin da Kasar ke da duwatsun ‘volcano’ fiye da 126.

- Mutanen Kasar fiye da 28,000 suka zo Kasar Faransa kallon ‘Yan Kasar ta su. Kenan kashi 8% na ‘yan Kasar sun zo mara ma yaran koci Lars Lagerback baya.

- Bari ta duwatsu, akwai tumaki fiye da 600, 000 a Kasar Iceland, wannan na nufin tumakin Kasar sun kusa ribanya mutanen Kasar har sau 2 a adadi.

- Wani abin da har yau duniyar kimiyya ba ta san amsar sa ba shine, a Kasar Iceland babu kwarin kiyashi. Wannan ba karamin abin ban mamaki bane.

- Daya daga cikin masu horar da yan wasan Kasar, Heimir Halligrimsson, likitan hakori ne. Shiyasa da Kasar ta doke Ingila, ‘Yan jarida suka yi ma Kasar Ingilar ba’ar cewa sun sha kunya wajen yaran likitan hakori.

 

 

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel