Chelsea ta sayi Michy Batshuay daga Marseille

Chelsea ta sayi Michy Batshuay daga Marseille

Chelsea ta sayi Michy Batshuay daga Marseille

– Michy Batshuayi ya koma Kungiyar Chelsea daga Olympique Marseille

– Dan wasan mai shekaru 22 yana buga ma Kasar Belgium lamba 9

– Michy Batshuay ne sayayyan farko na Chelsea bana

Chelsea ta sayi Michy Batshuay daga Marseille

Kungiyar Chelsea ta sanar da cewa ta saye dan wasan gaban Kasar Belgium daga Kungiyar Marseille ta Faransa mai suna Michy Batshuay. Kulob din Chelsea ta rubuta haka: “Wannan dan wasan mai cin kwallo, mai hanzari da karfi da aka fi sani da Michy Batshuay ya dawo Gidan Stamford Bridge da kwallo. Dan wasan dai gwarzon masanin raga ne, inda ya aje tuta a Kasar Belgium da kuma Faransa”. Kungiyar ta kara da cewa: “Michy Batshuay ya san kwallo, ya kware a yanka, nan take zai yanke ‘yan baya, ga kyau a sama, kuma ya iya rike kwallo…” Michy Batshuayi ya koma Kulob din Chelsea Michy Batshuay yana cikin tawagar kwallon kafar Kasar Belgium a gasar EURO 2016, a wasan san a farko Michy Batshuay ya jefa kwallo a raga, bayan da wani dan wasan na Chelsea ya dago masa kwallo, Hazard ne dai ya kai masa kwallon da ya ci, inda suka yi fata-fata da Kasar Hungary da ci 4 da nema.

KU KARANTA: AN KAI WA WANI DAN BARCELONA HARI

Michy Batshuay yace: “Ina farin cikin zuwa nan, wannan (Kulob din Chelsea) na daya daga cikin manya kungiyoyin turai da ma duniya. Ina fatar in taimaki kungiyar mu ci kofi a Stamford Bridge.” Michy Batshuay yace: “Hazard Eden da Courtois Thiabaut sun bani labarin Chelsea, gas hi kuma Antonio Conte na nan zuwa, wannan shine daidai lokacin da ya dace in zama dan kulob din Chelsea. Na kosa a dawo wasa, in fara bugawa.” A bayan nan dai Chelsea din ta salami, Falcao, pato da Amelia. Yanzu ta saye dan wasa Michy Batshuay.

Idan ana so a karanta labaran mu, sai a sauke manhajar mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel