Mummunan hatsari ya auku a hanyar Bauchi zuwa Kano

Mummunan hatsari ya auku a hanyar Bauchi zuwa Kano

- A kalla mutane 12 ne aka baiyana rasuwar su a wani mummunan hatsarin mota.                                                                                                                                    

  - Hatsarin da akace ya auku akan hanyar bauchi zuwa kano.                                                                                  

- Hatsarin dai ya farune da wata babban motan tanka dakuma kuma mota hilux wanda yayi sanadiyar mutuwan mutane.                                                                          

Hatsarin daya auku a hanyar Bauchi zuwa Kano yayi sanadiyar mutuwar mutane 12. Al'amarin ya aukune ranar Alhamis 30 gawatan yuni. Acewar majiyar mu, mutane 11 daga cikin wa'anda abun ya shafa suna aikin tsaro a wani sanannen ma'aikatan tsaro dake wajen garin wanda ake kira da Danga security, a lokacin da suke komawa garin Bauchi daga karamar hukumar Ningi inda abun ya auku a daidai kilomita 70 tsakaninsu da gari.

Mummunan hatsari ya auku a hanyar Bauchi zuwa Kano
hadarin motar

Commandan na Danga security outfit a bauchi Yusuf Hassan, wanda yake cikin wata mota sannan dayan motan da abun ya faru da ita tana gaban sa, suna tafiya a komboy suna masa rakiya. Yace abun ya farune da misalin karfe biyar na yamma a kyauyen Kafin liman, kan hanyar zuwa karamar hukumar Ganjuwa dake garin Bauchi. Duk da inda abun ya faru nan ma dai duk ganjuwa ne. Yace "Babu wanda yayi tsammanin haka zai fari.

Muna dawowa daga ningi zamuje bauchi ni kuma ina cikin motata, ita kuma hilux din tana cikin motocin dake mun rakiya, kilomita kadan ya rage mu karasa inda zamuje, wata tanka ta kubuce daga matukinta ta hade da Hilux dinmu inda yayi sanadiyar mutuwan mutanen mu 11 a take sannan shima direban tankar ya mutu.

Acewar sa ban taba ganin mutuwa irin wannan a tsawon rayuwata ba. Mutane 11 da suka rasu anyi musu sallan jana'izza kamar yadda addinin Islama ya tanada a masallacin juma'a na gwallaga kuma an birnesu a babban makabartar garin Bauchi dake kan hanyar zuwa Gombe.

KU KARANTA : An sace amarya kwana daya kafin aurenta

A cewar Premium Times, mai magana da yawun hukumar kula da hadura ta kasa (FRSC) dake Jihar Bauchi, Rilwanu Sulaiman ya tabbatar da faruwan al'amarin. Sulaiman yace abun ya farune da misalin karfe 5 na yamman, ranar alhamis, bayan da wata farar baban tanka mai lamba GLM- 534- XA tayi gaba da gaba da wata farar moto kirar Toyota Hilux wanda take cikin jerin motocin komboy na yan sintiri kusa da ningi akan hanyar su nazuwa Bauchi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: