Cinikin yan wasa 10 da sukafi daukar hankali

Cinikin yan wasa 10 da sukafi daukar hankali

Tun bayan da aka bude kasuwar cinikayyar yan wasa a kungiyoyi suka yi tayin kokari wajen ganin sun darje sun sayi rabon su tare da cigaba da ganin sun gyara kulob din su domin tunkarar kakar wasa mai zuwa.

Cinikin yan wasa 10 da sukafi daukar hankali

Kungiyoyi kamar su Liverpool, Arsenal da Baryen sun fara tasu cinikin tun kafin a fara gasar EURO 2016 yayin kuma da wasu kungiyoyin da yawa zasu yi nasu ne bayan gasar. Don haka Legit.ng mun zakulo maku cinikayya 10 da suka fi daukar hankali ya zuwa yanzu.

1. Renato Sanches: Kulob din Bayern sun ba kowa mamaki inda suka saye dan shekara 19 din daga Benfica a gaban Manchester a kan kudi $45m. Dan wasan dai zai nemi riga ne a tsakanin su Vidal, Xabi Alonso, Thiago Alcantara dama Joshua Kimmich.

 

2. Mats Hummels: Hummels dai ya koma kulob din sa na asali tun yana yaro bayan da ya shafe sama da shekaru 10 yan bugama Dortmund wasa yan zu dai zai koma Bayern inda zai rika buga baya tare da Boateng kamar dai yadda suke yi lokacin wasannnin kasashe.

 

3. Loris Karius: Kulob di Liverpool sun sayi sabon mai tsaron ragar ne daga Mainz akan kudi £4.7m har na tsawon shekaru 5. Ana sa ran zai maida Mignolet benci.

 

4. Ilkay Gundogan: Mancity suna bukatar yan wasan tsakiya daman to kuma sun fara sayen dan wasan Dortmund din gabaninn tashi Yaya toure da Fernando.

 

5. Marc Bartra: Bayan tashin Hummels zuwa Baryen, Dortmund sai suka siyo dan wasan baya na Barcelona don ya maye gurbin sa.

 

6. Eric Bially: Wannan dai shine dan wasa na farko da sabon mai horar war na Manchester Mourinho ya sawo daga kulob din Villareal kuma dan kasar Ivory Coast.

 

7. Miralem Pjanic: Kulob di Juventus yana ci gaba da kara karfi bayan da siyo wannan dan wasan daga AS Roma. Dan kwallon Bosnian ya zura kwallaye 10 sannan kuma ya taimaka wajen wasu 12 a wasanni 33 da ya buga kakar wasannin da ta wuce.

 

8. Joel Matip: Duk da dai shi wannan an gama cinikin nasa ne tun tuni amma yanzu zai tafi kulob din na Liverpool don ya taimaka wajen dinke barakar dake bayan ta su. Shi dai dan kasar Kamaru ne kuma daga kulob din Schalke O4.

 

9. Sofiane Feghouli: kulob din West Ham ne dai suka siyo dan wasan daga Valencia har na tsawon shekara 3 a kan wasu kudi da basu fada ba.

 

10: granit Xhaka: Ma goya bayan Arsenal dai tuni har sun fara murna don kuwa sunyi babban kamu da siyen wannan hazikin dan wasan na tsakiya daga Germany.

Asali: Legit.ng

Online view pixel