Tashin Hankali: Gawa ya shigo kotu
– Wani abin tashin hankali ya faru kotun Majistaren Krugersdorp yayinda gawa ya shigo kotu
– Duniya na zaton mutumin ya mutu a hadarin gobarar hutu a shekarar 2015
– Har yanzu ba'a gushe ana binciken mutuwan sa ba
Wani dan shekara 31 da ake tunanin ya mutu a wata hadarin gobarar mota a watan disamba 2015 ya shigo kotu katsam. Hadarin ya faru ne a ranar 16 ga watan disamba a garin krugersdorp, kakakin yan sanda, appel Ernst ya ce.
KU KARANTA:Manyan laifuka 6 da ake aikatawa a Najeriya
Jaridar news 24 ta bada rahoton cewa an boye sunan shi a halin da jami'an yan sanda na gudanar da bincike. Ya kasance yana gurfana ne a kotun krugersdorp da laifin zamba, kuma a wani kotun frew state da laifin kisa. Ashe bayan hadarin, ya gudu free state,shi yasa aka fara binciken shin gawar wa aka samu a wurin hadarin . Kotun Majistaren Krugersdorp ta dakatar da karan zuwa 6 ga watan yuli.
A wani labari mai kama da haka, wata mata mai suna Noela Rukundo, wacce ake tunanin ta mutu, ta tayar ma mutane da hankali yayinda ita ma ta halarci jana'izar ta gab da a gama. Har lokacin da ta dawo, kawayen Rukondo da dangin ta basu sam abin da ya faru ba, shin ita ce ko fatalwa ta ne?.
KU KARANTA : Jami’an tsaro na farin kaya sun cafke yan gidan Yarin Kuje
Abun ya faru kwanaki 5 da suka gabata,ashe mijin ta,Balenga Kalala, ya aika yan kisan kai su kashe ta, bayan sun yi zamantakewan aure na shekaru 10 . Allah mai iko, yan kisan kan sun fada ma balenga cewa sun kashe ta ,alhalin basu kashe ta ba, kana ma sai da kara musu kudi domin kamalla aikin.
Asali: Legit.ng