Manyan laifuka 6 da ake aikatawa a Najeriya

Manyan laifuka 6 da ake aikatawa a Najeriya

-Hukumar hana yima tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC a takaice na  da zarra wajen zakulo masu laifi ta kuma gurfanar dasu gaban shari'a 

-Haka kuma hukumar tayi tasiri wajen fadakar da 'yan Najeriya game da illar cin hanci da rashawa, da kuma yadda za'a iya kauracema laifin

Manyan laifuka 6 da ake aikatawa a Najeriya
efcc

Hukumar EFCC ta zayyana manyan laifikkan wadanda suka zamar ma kasar karfen kafa wajen ci gaban tattalin arziki. Shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu yana yima hukumar kwaskwarima domin mayar da hukumar zama wadda ta dauki nauyin da ke kanta ta muhimmanci.

Wadannan laifuka sune kamar haka:

Laifin daya shafi tattalin arziki.

Laifin ya shafi gurguntar da arzikin gwamnatin jiha ko ta tarayya. Ya jibanci laifuka irin su fasa bututun mai, satar mai, kin biyan haraji da sauransu.

Wannan laifikkan sun shafi amfani da kudi ba bisa ka'ida ba ko kuma abubuwa da suka danganci haka, irin su cekin kudi, cekin draft, bada ceki na karya da sauransu.

Ya shafi yaudara da niyyar cuta ta hanyar amsar kudi domin wata sabgar kasuwanci, ko soyayyya ko kwangila da sauransu.

Shigar da haramtattun kudade cikin sabgar kasuwanci yadda zasu kasance kamar an wankesu.

Amfani da tashin hankali, taratsi da barazana domin cima wani guri na siyasa, ko addini ko manufa.

Sun shafi amfani da na'ura mai kwakwalwa ko kwatankwacin haka domin yin laifi

Shagunan da ake shiga yanar gizo dole su yi rajista da EFCC domin su san abinda suke cike, su kuma kaucema laifikkan yanar gizo.

KU KARANTA:Kotu ta garkame tsohon gwamna a kurkukun Kuje

 

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: