Falcao da wasu ‘yan wasa 2 za su tattara su bar Chelsea

Falcao da wasu ‘yan wasa 2 za su tattara su bar Chelsea

– ‘Yan wasa 3 za su tattara kayan su, su bar Stamford Bridge.

– Ciki har da Alexandre Pato, wanda ya zo aro daga Kungiyar Corinthians a Janairun bana.

– Antonio Conte ya sayo dan wasan da ya san ragar nan, Michy Batshuay.

Kungiyar Chelsea ta shirya yin waje da ‘Yan wasa 3 wadanda suka hada da; Radamel Falcao, Alexandre Pato da kuma gola Marco Amelia. Dan wasa mai shekaru 26, Alexandre Pato ya zo Chelsea ne aro daga Kungiyar Corinthians na Brazil a watan Janairun wannan shekara, inda yaci kwallon finariti wasan sa na farko da ya buga da kulob din Aston Villa, a wasan Chelsea ta doke Aston Villa da ci 4 da nema. Kana ya buga wasa da Swansea, inda Chelsea ta sha ci 1 mai ban haushi. Wasan Swansea din ne dai kadai wasan da aka take da dan wasa Pato. Radamel Falcao zai koma kungiyar sa ta AS Monaco, ko da ma can, aro ya zo shima. Shi kuwa mai tsaron raga, Marco Amelia ya zo ne a matsayin mai canzan Thibaut Courtois, sai dai bai samu bugawan ba, yanzu haka, Marco Amelia ba shi da kulob a kasa.

Falcao da wasu ‘yan wasa 2 za su tattara su bar Chelsea

 

 

 

 

Kungiyar Chelsea dai ta amince da sayan wani dan wasan gaban Marseille na Faransa, Michy Batshuayi. Chelsea za ta saye dan wasa Batshuayi ne a kan farashi fam miliyan £33. Rahotanni suna zuwa mana cewa, dan wasan Marseille din zai sa hannu kan kwantiragin shekaru 5 da Chelsea. Zai koma London da buga kwallo muddin an yi masa gwaji. Idan kuwa har wannan ciniki ya tabbata, Kungiyar Marseille za ta biya tsohon kulob din Batshuayi, Kungiyar Standard Liege kaso 35% cikin abin da ta samu, akwai yiwuwar Kulob din na Kasar Beljium ta tashi da fam miliyan 11.5 daga ciki, domin wata yarjejeniya da suka kulla a baya.

Dan wasan mai shekaru 22 a duniya, ya jefa ma Marseille kwallaye fiye da 20 a gasar wannan shekarar, ko a ranar da aka kara a Gasar EURO tsakanin Kasar sa ta Belgium da Hungary, ya jefa kwallo guda a lilo, bayan ya canji Romelu Lukaku.

 

 

 

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng