Mutane fiye da 300,000 suka nemi aikin EFCC
– Hukumar Yaki da cin Hanci da Rashawar Najeriya ta EFCC tace ta samu fiye da mutane 300,000 masu neman aiki.
– Hukumar ta EFCC dai tace mutane 750 kacal za ta dauka aikin.
– Daraktan yada labarai na hukumar, Mr. Osita Nwaja yace za a dauki ma’aikatan ne domin kara kaimi wajen Yaki da cin hanci da rashawa a Kasar.
Mutane fiye da 300,000 suka nemi aikin EFCC, Hukumar dai ta EFCC ta tallata cewa za ta dauki ma’aikata 750 a baya. Osita Nwaja wanda shine Daraktan yada labarai na hukumar ta EFCC ya bayyanar da hakan a ranar Laraba, 29 ga watan Yuni ga manema labaran Kasar (NAN) a Jihar Enugu. Osita Nwaja ya sanar cewa za a bi ka’ida ne wajen daukar ma’aikatan, kuma kawo 26 ga wannan watan, za a kammala matakin farko na diban ma’aikatan.
KU KARANTA: AN KONA WANI MUTUM KURMUS A DELTA
Daraktan ya sanar da cewa mutane fiye da 300,000 suka nemi aikin, sai dai mutane 750 kacal za a dauka a hukumar. Za a dauki kananan ma’aikata, da na mataki na tsakiya da kuma manyan ma’aikata. Nwaja yace za a fi bada hankali wajen daukar kananan ma’aikata saboda su san makamashin aiki. Jami’in na EFCC ya bayyana cewa za a dauki mafi cancanta a Hukumar. Yaki da rashawa wani abu ne da ya zama dole a Kasar nan, dole muyi nasara wajen yaki da cin hanci da rashawa. Shiyasa muke ta daukar ma’aikata domin muyi aiki da kyau Inji Daraktan Hukumar.
KU KARANTA: BA ZA MU YARDA 'YAN BINDIGA SU HALLAKA MU BA, INJI YARBAWA
Idan ba a manta ba Hukumar ‘Yan Sandan Kasar ita ma ta sanar da cewa ta samu fiye da mutane 700,000 masu neman aiki na ‘Yan sandar Kasar. Daraktan yada labarai na hukumar Mr. Ikechukwu Ani ya bayyana cewa mutane 202,427 suna neman matsayin mataimakin sufiritanda (watau ASP), sannan 169,446 suna neman matsayin Sufeta na Cadet, sai kuma mutane 333,479 suna neman matsayin kurtun ‘Yan sandan.
Asali: Legit.ng