‘Yan Boko Haram sun faffado daga tsauni sun mutu

‘Yan Boko Haram sun faffado daga tsauni sun mutu

‘Yan Boko Haram sun faffado daga tsauni wajen fada da Sojojin Najeriya

‘Yan Boko Haram sun faffado daga tsauni sun mutu

 

 

 

 

 

 

Wasu ‘Yan Boko Haram sun faffado daga tsaunuka yayin da rundunar Sojojin Najeriya ta kai masu wani hari a Gwoza, Jihar Borno. Mai magana da yawun bakin sojojin Kasar, Kwanal Sani Kukasheka Usman ya bayyana haka a ranar Laraba 29 ga watan Yuni. Yace duk da cewa ba za a iya bayyana yawan wadanda aka kashe ba, amma an kai ma ‘yan ta’addan da ke buya a Kauyukan Ngoshe da Gava wani mummunan hari. Ga abin da jawabin nasa yake cewa:

“A yau Talata 28 ga watan Yuni 2016 ne runduna ta 121 na hadin gwiwa, bataliya ta 26, hade da wasu ‘yan rundunar kato-da-gora daga Gwoza suka kai wani mummunan hari don karasa ragowar ‘Yan Boko Haram din da suka rage a Kauyukan Gava da Ngoshe, na kusa da tsaunukan Gwoza. An kai farmakin ne domin karasa gamawa da  ta’addan 'Yan Boko Haram da ke boye saman tsaunukan yankin da kuma kwato mutanen da ‘Yan ta’addan suka kama. Sojojin saman Najeriya da kuma Sojin Kasar Kamaru suka taimaka ma rundunar sojin Kasan na Najeriya wajen basu kariya ta sama da kuma bayanan abokan yaki. A hanyar zuwa Ngose, rundunar soji ta gamu da ‘Yan ta’adda, wanda da taimakon rundunar sojin sama, aka gama da su. Ko da cewa ba a san takamaiman yawan wadanda aka kashe ba, amma an ga da yawan su suna fadowa daga saman tsaunukan, babu mamaki wasu sun tsere bayan sun sha harbi daga Jiragen Yakin Sojojin saman Najeriya”

Game da kayan da aka gano akwai: Gurnet na RPG 1, Bam na RPG 4, Bindiga mai jigida 1, Bindigogin AK-47 3, Wata Bindigar FN. Sauran abubuwa sun hada da: Wata Karamar Bindigar hannu, bindigogin toka, harsashi na NATO guda 243, da wasu harsashen kuma. Har way au, an gano: Bindiogoin AK-47 guda 2, Jigida, Gidan Harsashi 18 na bindigar MI16, Wasu Manyan bindigogi 3, wayar salula da layin waya da kuma kayan soji (khaki). Sai kuma: Babura, tutoci, da Motar ‘Hilux’.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng