Ido- da ido: Ana cacar baki tsakanin Buhari da Saraki

Ido- da ido: Ana cacar baki tsakanin Buhari da Saraki

-Fadar shugaban kasa ta shiga cacar baki da Bukola Saraki ranar Litinin 27 Yuni 2016.

-Bukola Saraki ya zargi cewa wasu 'Yan baranda sun mamaye gwamnatin Buhari

-A nata maida martanin, fadar shugaban kasar tayi watsi da maganar shugaban majalisar dattawa, tana mai cewa maganar bata da kan gado.

-Ike Ekweremadu yace idan kura ta lafa, 'yan Najeria zasu ankara cewa shari'ar da ake masu ba ta da ma'ana.

Ido- da ido: Ana cacar baki tsakanin Buhari da Saraki
buhari da saraki

Manyan jaridun Najeria ranar Talata 28 Yuni 2016 sun maida hankali a kan cacar baki da ake tsakanin shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da fadar shugaban kasa a kan shari'ar da ake ma Ekweremadu da Saraki kan zargin yin aiki da dokokin majalisar na jabu.

Jaridar Guardian ta ruwaito cewa an gurfanarda Saraki da Ekweremadu a wata babbar kotu dake cikin  garin Abuja a kan zargin kirkiro dokokin majalisa na jabu. Ana kuma tuhumar tsohon kakakin  majalisar Alhaji Salisu Abubakar Maikasuwa tare da kakaki mai rikon gado, Benedict Efeturi tare da shugaban majalisar da mataimakinsa . Ana zarginsu da buga dokokin jabu na kaidojin aiki na majalisar wadanda aka yi aiki da su aka zabi Saraki da Ekweremadu ranar 9, Yuni 2015 a matsayin shuwagabannin majalisar. Bayan An karanta masu zargin da ake masu, wanda suka amsa da cewa basu da laifi, lauyoyinsu sun bukaci da a bada belin su, wanda kotu ta amince da shi

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa an dauki tsatsauran matakan tsaro a harabar kotun.

Jami'an tsaro dauke da makamai sun hana 'yan jarida  masu daukar hotuna shiga kotun, abin da ya jaza korafi daga 'Yan jaridar. Sai da lauyoyi suka sa baki kafin 'yan sandar su amince ma 'yan jaridar shiga kotun. Magoya bayan Saraki sun yi tururuwa zuwa kotun domin gani da idonsu.

KU KARANTA : Yan Najeriya sun koka dangane da zargin da ake yima Saraki

Jaridar Daily Sun ta ruwaito cewa bayan an bada belinsa, ya zargi wadansu masu fada aji da kwace gwamnatin Buhari. A cewar Saraki, Buhari ba shine ke mulki ba amma wasu 'yan baranda ne suka kwace gwamnatin A cikin sanarwar da ya sama hannu, yana mai cewa "abinda ya fito karara shine akwai gwamnati cikin gwamnatin Shugaba Buhari wadda ta amshe mulki domin biyan bukatun su na kansu. A cewarsa, shirye yake da ya tafi gidan jarun idan yin hakan shine sakamakon jajircewar da yayi kan hana wasu 'yan tsirari yima damokradiyya Karan tsaye domin bukatun san zuciyyarsu.

Ya gargadi gwamnati tare da jam'iyyar All Progressive Congress da su sake tunani game da abinda suke ma majalisa ko kuma su fuskanci rashin amincewar 'yan Najeria. A nashi maida martanin, mai ba shugaba Buhari shawara kan jaridu da labarai Femi Adesina ya bukaci Saraki da ya fadi sunayen mutanen da yake magana. Yace idan shugaban majalisar ya bada bayani mai gamsarwa da za'a fi daukar maganar sa da muhimmanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng