Mikel Obi na shirin barin Chelsea
-Mikel na shirin kawo karshen zamansa na shekaru a Chelsea
-Kyaftin din Super Eagles na iya barin Chelsea domin ya bugawa wani kulod da ke rukunin farko a kwallon kafa
-Ejan din sa bai samar masa gurbi ba tukunna
Akwai alamu masu karfi da ke nuna cewa kyfatin din Super Eagles John Mikel Obi, na shirin sauya sheka daga Chelsea wannan bazarar bayan shafe shekara 10.
A cewar shafin Goal.com na Intanet, Mikel na shirin barin Chelsea ne domin ya samu damar bugawa wani kulop din da ke rukunin farko na kwallon kafa, kuma hakan ya biyo bayan zuwan kociya Antonio Conte dan kasar Italia ne.
Sai dai duk da kasancewar sa da ‘yan shudin gida, tun shekarar 2006 bai kare ba, saboda yana da ragowar shekara guda a yarjejeniyarsa da kulop din, har yanzu ba’a ba shi tabbacin ci gaba da wasa da su ba, kafin shiga sabuwar kakar wasanni.
KU KARANTA: NFF sun amince da Paul Le Guen a matsayin mai horaswa
Mikel ya taba yin magana a kan makomarsa a Chelsea, bayan wasan Najeriya da Misira a watan Maris da ya wuce, a inda ya fito karara ya nuna damuwarsa, ya na mai cewa; “dole ne in ci gaba da wasa, domin ba zan yarda da zaman dumama benchi kamar yadda na yi a baya ba.”
Legit.ng na iya tunawa da cewa Chelsea ta fitar da jerin ‘yan wasan da za ta ci gaba da yi mata wasa da kuma wadanda za ta kyale a kakar wasanni na shekarar 2016 zuwa 2017, ciki har da Mikel da Kenneth da Omerou wadanda ke cikin wadanda za su ci gaba da buga mata wasa.
Asali: Legit.ng