Kannywood sun yi wa ‘yar cikinsu gata

Kannywood sun yi wa ‘yar cikinsu gata

-Masu shirya fina-finan Hausa da aka fi Kannywood sun yi wa daya daga cikinsu gidauniya

-Fati Suleiman tauraruwa shirin fina-finan Hausa a da, na fama da sankara mahaifa.

-‘Yan fim su yi mata agaji a in da suka taimaka a ka yi mata aiki

Fatima Suleiman wata ‘yar shirin wasa wacce ta game da larurar mahaifa ta samu agaji daga abokan sana’arta a Kano.

Kannywood sun yi wa ‘yar cikinsu gata
Mai jinya Fati Suleiman tare da Halima Adamu a gadon asibiti bayan an yi mata aiki

 

A wani labari da Jaridar Rariya ta buga a shafinta na sada zumunta da muharawa na Facebook, ta bayar da labarin cewa jarumar na fama da wata cuta a mahaifarta wanda ta kai tsananin da sai an yi mata aiki a wani asibiti a Kano, amma ita da mijinta ba su da halin biyan N200,000.

Wannan labari ya sa ‘yan Kanywood ciki har da mawakiya Fati Nijar da Adam A zango, da Rahama Sadau  Sadau da sauran su, suka yi mata gidauniya a inda aka samar da kudin aikin.

Rahotanni na cewa an yi Fati aikin tiyatan ne a mahifarta a ranar Asabar da misalin karfe 3:00 na dare ta na kuma samun sauki.

KU KARANTA: Tirkshi : Namiji da ciki

Wani tsohon dan jarida Ibrahim Sheme ne ya fara ba da labarin rashin lafiyarta a shafinsa na sada zumunta da muhawara na Twitter a intanet, kafin ‘yan Kannywood din su kawo mata dauki. Fati Suleiman ta yi aure ne a lokacin da ta ke tashe a shirin fina-finan hausa a shekarun baya, ta na kuma zaune da mijinta a Kano.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel