Ashe Biri yayi kama da Mutum:An kama Sakataren PDP

Ashe Biri yayi kama da Mutum:An kama Sakataren PDP

-   An kama tsohon mukaddashin Sakataren jam'iyyar PDP ta kasa ,Chif Onwe Solomon Onwe a Jihar Ebonyi da laifin mallakan bindigogi da garkuwa da mutane.

-  Hakan ya bayyanu ne a wata jawabin da ofishin yan sandan Jihar Ibonyi ya saki a ranar lahadi, 26 ga watan yuni, kuma aka ba manema labarai.

Game da rahoton Jaridar Leadership,  an kama Onwe ne domin yunkurin sakin wani mai laifi da ke karkashin bincike.

Yayinda ya ke magana da manema labarai, kakakin yan sandan Jihar Ebonyi DSP George Okafor, yace Onwe ya dade yana daukan nauyin wadansu mugayen ‘yan daba domin tayar da hankalin mutane ta hanyar garkuwa da mutane da yin fashi. Ya ce:

Kwanaki, la'alla kun samu labarin kisan wan dan yanda , wani Sergent a watan afrilu a hanyar Abakaliki/Enugu inda akayi fashi da makami. ‘yan fashin sun dade suna tayar da hankalin mutane,  su ne sukayi garkuwa da wani mai suna hilary a garin Umuoghara, karamar hukumar Ezza maso arewa, munyi iya bakin kokarin mu kwato shi amma an samu musanyan wuta tsakanin mu da yan fashin, wanda ya kashe wani mai suna Ejike dake tuka wata motar da aka kwace daga hannun mai shi kwanaki a layin conbemt a Abakaliki.

 “Abinda ya kawo Onwe.S.Onwe kenan, Yayinda muke gudanar da bincike , mun kama Emeka Akonuche, wanda dan fashi ne kuma masu garkuwa da mutane, mun kama shi a Nkakiki , a Abakaliki.Daga baya Emeka ya arce daga ofishin yan sanda, sai muka je muka kamo matarsa  aka kawo ta ofishin yan sanda domin yi mata tambayoyi, a lokacin, an samu wadanda suke son a amsan belin ta.

KU KARANTA:  Jam’iyyar PDP ta dakatar da wani dan takaran Gwamna

“Bugu da kari,  mun kama wani kuma, sai muka lura cewa, daya daga cikin mutanen da ke son a bata beli abokin mu ne, Insfecto Francis Inyeka tare da wani Christian Chinedu Ogba daga Ohaukwu. Su biyu suka dage a saki matan , kuma muna ta lura da su.  da muke lura da motsin su, sai muka gano cewa dukkansu yan kungiyan yan fashi daya ne , kuma mun kama su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: