Uwargida ta kashe Mijinta kan bin Matan banza

Uwargida ta kashe Mijinta kan bin Matan banza

Yan sanda sun damke wata mata a garin Benue da ta kashe Mijinta, ita da kannenta maza ne suka hada kai suka ma Mijin dukan kawo wuka dalilin yawan bin Matan banza da yake yi. Sa’annan suka wurga gawar sa cikin tafkin Katsina-Ala.

 

Uwargida ta kashe Mijinta kan bin Matan banza
An kama matar da kashe mijinta

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Mijin matar mai suna Godwin Abuul wanda ke koyarwa a tsangayar koyar da was an kwaikwayo na makarantar kwalejin ilimi da ke garin Oju a Jihar Benue an kashe shi kuma aka wurgar da gawan sa a tafkin Katsina-Ala. Wani majiya da baiso a bayyanr da sunansa wanda dangi ne na kusa dasu ya fadi cewa Mutumin ya bace ne tun sati 2 da suka wuce kafin bincike ya tabbatar da gaskiyar lamarin day a faru.

Majiyar ya kara da cewa “shi Goddy malami ne a Kwalejin Ilimi da ke garin Oju, yana tafiya zuwa Oju daga Gboko duk sati, daga nan sai ya dawo hutun karshen mako don ya kasance tare da matarsa da yaransa. daya dawo daga Oju  sati 2 da suka wuce ne sai yace za shi Katsina-Ala, daga nan bamu kara jin duriyar sa ba. An sanar da bacewarsa ga Yan-sanda inda suka bazama nemansa, cikin ikon Alla sai ga shi an samu rigarsa da ke sanye jikinsa a wancan lokaci a jikin wani Saurayi, nan da nan Yan-sandan Gboko suka kama shi.

Bayan dan Samarin ya sha tambayoyi ne sai ya tabbatar ma Yan-sanda yadda aka yi ita Matar ta kashe Muyumin tare da hadin kan Kannenta.” “Ikirarin da yayi ne ya sa Yan-sanda Gboko kama mutane da yawa, ciki har da Matar mamacin kuma uwar yayansa, amma yanzu an mika batun ga Babban ofishin yan sanda na Makurdi, a yanzu haka Matar da gama zayyana ma Yan-sanda bayani akan duk abin da ta sani.”

“Mun samu labarin, ta yi ikirarin cewa Kannenta Maza ne suka yi ma Mijin nata duka tsiya a dalilin zargin sa da suke da bin Matan banza, amma ba wai sunyi niyyar kashe shi bane, bayan sun kashe shi ne, shine suka yard a gawan nasa a rafin Katsina-Ala kuma suka siyar da motansa kirar Honda akan naira 650,000, a cikin kudin ne aka ba Matar naira 400,000 a matsayin kason ta.”

“Maganan da nake maka yanzu, Yan-sanda da masu iyo suna nan suna neman gawar mamacin a cikin tafkin Katsina-Ala, amma muna shakkar ko za’a ga gawar, wata kila ma kifaye sun cinye shi.”.

Mai magan da yawun Yan-sandan ya tabbatar da afkuwar lamarin, amma yace ba shi da cikakken bayani, “ina sane da lamarin, amma ban kai ga samun cikakken bayani akai ba daga DPO saboda ba’a riga an kawo wadanda ake zargin ba garin Makurdi. A yanzu dab a zan iya tabbatar maku ka Matarsa tana da hannu ba, har sai na samu cikakken bayani”

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng