EFCC ta sake damke Saidu Dakingari

EFCC ta sake damke Saidu Dakingari

-Hukumar EFCC ta sake kama saidu dakin gari a karo na biyu saboda hannun shi a cikin raba naira miliyan 450 na yakin neman zabe

-  An ce Dakingari yayi bayanin yadda aka karkatar da kudi naira miliyan 550 na Jihar Kebbi zuwa jam’iyya sa ta PDP

-  EFCC ta kama Dakingari a watan oktoba 2015 akan kudin Jihar Kebbi naira biliyan 3.8 da aka sace

Hukumar hana al mundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zaman kasa watau EFCC ta sake kama Tsohon gwamnan Jihar Kebbi ,Sa’idu Dakingari. Jaridar Thisday ta bada rahoto.

EFCC ta sake damke Saidu Dakingari

Game da rahoton, EFCC na cikin yi masa tambayoyi a ofishin su na Jihar Kano akan hannun sa a cikin kudi naira miliyan 450 na yakin neman zaben PDP. Haka zalika sun tambaye Dakingari  yayi bayanin wani kudi naira miliyan 550, kudin jihar kebbi da ya karkatar zuwa yakin neman zaben tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan.

A wani jawabin da Mr. Medard Ehimika, shugaban yada labarun hukumar EFCC, shiyar Jihar Kano, an samu cewan dakingari na bada hadin kai wurin binciken.

KU KARANTA: EFCC na tuhumar jami’an NNPC a gaban kotu

A watan oktoba na shekaran da ya gabata 2015, EFCC ta kama Dakingari akan tuhumar sa da akeyi na sace kudi naira biliyan 3.8 daga asusun Jihar Kebbi. An daure a hedkwatan EFCC na awanni da dama kafin aka sake shi.

Dakingari dai sirikin tsohon shugaban kasa,Umaru Musa Yar’adua ne. Kwanan nan, EFCC ta kama matar tsohon Gwamnan, Hajia Zainab. Ana tuhumtar ta da taya mijin ta sace kudi naira biliyan2. Dakingari yayi shugabancin jihar kebbi ne karkashin jam’iyyar PDP daga 2007 zuwa 2015

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel