Mutanen Neja-Delta ba su aminta da Buhari ba – Inji Orubu
- Mutanen Neja-Delta ba su aminta da Gwamnatin Buhari ba – Inji Orubu
– Cif James Orubu yace badakalar Neja-Delta na faruwa ne domin mutanen yankin basu yarda da Shugaba Buhari ba.
– Orubu kuma yake cewa tsagaita wutan da soji suka yi abu ne mai kyau.
– Yace wasu matakan da gwamnati ta dauka ya jawo kara tashin wutar rikicin, amma za a iya kashe ta.
Cewar Cif James Orubu, sulhu ne abin da yafi dacewa ayi wajen kawo kan matsalolin yankin na Neja-Delta. Yake jaddada maganar yunwa, yace aikin gwamnati ne ta samar da abinci, amma ba ta yi ba. Akwai yunwa ko ina a Kasa, ga kuma Naira tayi kasa. Ba a dade da gama wahalar mai ba, irin wahalar da ba mu taba gani ba. Kuma ga shi an kara farashin man fetur din, kuma aka bi mu da karin farashin wutan lantarki. Kasuwanci ya tsaya cak a Najeriya, babu kudin jari, kudin kasar na cikin wani mawuyacin hali, ‘yan kasuwan waje basu shigowa Kasar.
KU KARANTA: Tension in Lagos: Gunmen attack, kill many in Ikorodu
Dole gwamnati ta duba matsalolin da ya shafi wannan yanki (Na Neja-Delta) ta ga yadda za ta shawo kan su. Akwai bukatar mutanen wannan yanki su ji cewar, eh akwai gwamnati mai aiki. Da yake jawabi kan sulhu da ‘yan Niger Delta Avengers da kuma Tompolo yace: “Tompolo yayi maza yayi amfani da wannan dama ya sasanta da Shugaba Muhammadu Buhari. Lauyoyin sa su hanzarta. Hukumar EFCC kuma tayi ta gama aikin ta ba tare da son kai da nuna bambanci ba”
Ya kamata Shugaban Kasar mu ya sani cewa Tompolo shi ya shawo kan matsalar tattalin arzikin kasar nan lokacin da aka shiga wani mawuyacin hali zamanin Shugaba ‘Yaradua. Shi yayi tsayin daka aka wajen ganin an daina satar man kasar nan. Wajen haka ne Marigayi Shugaba Ummaru ‘Yaradua ya jinjina masa domin yana barayin gwamnatin Tarayya, sanadiyyar haka ya samu makiya da dama, wanda yanzu suke adawa da shi. Saboda haka gwamnati tayi amfani da wannan dama, ta daina kwarzabar sa (Tompolo) domin a samu ya ba mutanen yankin hakuri, su janye wukar su.
Yake ganin cewa gwamnati ta duba maganar tsaron bututan mai da ta kwace daga hannun wadannan mutane, hakan ya jawo da daman su suka zama basu da aikin yi. Wannan abu bai masu dadi ba. Yace bai yi mamaki ba da ya ga mutanen sun dauki makamai, ya kara da cewa yana da kyau gwamnati ta rika shawara irin haka kafin daukar mataki.
Orubu yace wannan rikici zai kawo matsalar a alakar da ke tsakanin Urhobo, Ijaw da Itsekirin da ke zama a yankin cikin lumana. Yace sulhu kadai zai kawo karshen matsalar ba karfin soji ba. Dole gwamnati tayi sulhu da tsagerun da kuma manyan yankin.
Kawo yanzu dai gwamnatin tarayyan da tsagerun Neja-Deltan wanda suka hada da Niger Delta Avengers (NDA) sun yarda da tsagaita wuta har na wata daya.
Asali: Legit.ng