Aregbesola ya fito yayi magana akan Hijabi

Aregbesola ya fito yayi magana akan Hijabi

- Gwamna Aregbesola ya fito ya amsa tambayoyin da ake masa akan hayaniyar Hijabi a jihar

-Yace gwamnatinsa ba ta umurni dalibai mabiya addinin Islama su sanya Hijabi ba    

Aregbesola ya fito yayi magana akan Hijabi
gwamna argbesola

Gwamnan Jihar Osun, Rauf Aregbesola ya fito yayi amsa tambayoyin jama’a akan hayaniyar hijabin da ya taso a Jihar, ya ce masu cewa shi ya umurni dalibai mabiya addinin islama da su sanya hijabi su kawo hujja akan tuhumar da suke mai. Gwamnan yayi Magana ne a wani taron tabbatar da cigaban ilimi a babban birnin jihar,Osobgo. Ya bayyan cewa gwamnatinsa bata umurci dalibai mabiya addinin islama da su sanya hijabi ba a makarantun gwamnatin jihar.

Ya ce “Da na yarda da hijabin, mabiya adinin islama zasu je kotu?  Wannan ba tifka da warwara ne? Shin wai laifi ne kasancewa na musulmi,ko dan nayi kokarin in zama musulmin kwarai,shine duk abinda ya faru a dauka ni nayi? Ban tunani ya kamata a dinga min karya ba”

Mr Aregebesola ya kara da cewa shirye-shiryen da ya kawo ma ma’akatan ilimi na daga cikin shawaran da muke yanke daga shigowar mu gwamnati.

“ Dokokin mu ba su da alaka da addini, yan adawa mu na tifka da warwara ne kawai. Zaben mataimakiyar gwamna ma kadai ya isa hujja, ai mai tsatsauran addini kirista ce kafin in dauke ta. Duk abinda muka zantar a ma’aikatan ilimi, munyi shi ne bisa ka’idan shirin ilimi. Kuma nace, ban umurci kowa da ta sa hijabi ba , ina kalubalantar ko waye da ya kawo hujjan cewa nayi hakan.”

ku karanta:Aregbesola yayi hattara akan hayaniyar Hijabi – CECCUR

Bayan yanke hukuncin kotu, dalibai mabiya addinin Islama sun fara sanya Hijabi zuwa makarantu, amma hakan ta kawo hayaniya ,a yayinda shuwagabannin mabiya addinin Kirista suka nuna rashin amincewan su da hukuncin kotun, hakan yasa wasu dalibai mabiya addinin kirista suka fara sa kayan coci zuwa makaranta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng