Yar wasan kwaikwayon Nollywood ta auri bature
- Yar wasan kwaikwayon Nollywood ta auri bature.
- Hamshakiya kuma dadadda ‘yar wasan fim din Najeriya Chika Chukwu wanda ta fito a matsayin Jumoke a wasan Fuji House of Commotion ta auri bature.
Chika Chukwu da mai gidan ta Brian Ahern.
Bayan ta kammala wasan kwaikwayon ta na karshe, Chika Chukwu ta dauki dogon lokaci ba a gan ta ba a fili. Daga baya ta dawo cikin fim din Rita Dominic. Kwanan nan tayi hira da jaridar nan ta The Nation, inda ta bayyana abubuwa da dama, wanda suka hada har da maganar auren ta da wani bature.
Ga abin da hirar ta Chika Chukwu ta kunsa
An samu ganin ki kwanaki cikin kayan amare a birnin Landan, ana tunanin kina wani fim din ne ko ya abin ya ke? Ba wasan kwaikwayo nake yi ba a Landan. Na dai yi aure ne a shekaran baran, cikin watan Agusta.
An ce ‘Mace allurer cikin ruwa, mai rabo ka dauka.’ Waye mai wannan rabo haka? Kuma ina kuka hadu?
Abin da zan ce ga mu nan duk cikin jin dadi. Yadda muka hadu kuwa shi ya gano ni, sunan sa Brian Ahern, mutumin Kasar Ireland ne… Kuma yana zaune a Landan. Kuma shi ba dan fim bane. To, kun ji!
Ke kuwa meyesa kika auri kwara, dan kasar Ireland?
Duk mun yi wannan tunanin. Ni ma ban taba kawo hakan a rain a ba.
Yanzu aure zai sa ki tare Landan da zama kenan?
Ai dama can nayi karatu a nan, bugu da kari, ina da dangi a nan. Na saba zama nan in yi yan watanni tun bay au ba. Kwanan nan muka yi aure, yanzu dai muna tare kafin kowa ya koma wajen aikin sa. Muna iya kokarin mu. Kullum ina kan zirga-zirga tsakanin Legas da Landan.
Me kuma za kice ya faru a rayuwar ki cikin shekaran nan, ganin kin bar Nijeriya?
Sai in ce, Ni dai na samu me sona, kuma nima nake son sa. Ba kai na za a far aba, kuma ba kai na za a daina auren farin fata ba.
Asali: Legit.ng