Ajumogobia ya ki amsa gayyatar ‘Yan Neja-Delta

Ajumogobia ya ki amsa gayyatar ‘Yan Neja-Delta

- Henry Ajumogobia ya ki amsa gayyatar ‘Yan Neja-Delta

– Henry Ajumogobia ya bayyana cewa ba zai tsaya a matsayin mai tattaunawa da Gwamnati ba da bakin ‘Yan Neja-Delta

 – Yana cikin wadanda aka zayyana za su tattauna da gwamnatin tarayya.

 – An gamu da fashe-fashen bututun mai daga hannun tsageru a yankin cikin ‘yan kwanakin nan.

Ajumogobia ya ki amsa gayyatar ‘Yan Neja-Delta
Niger Delta Avengers

Shirin tattaunawar lumanan ya samu tasgaro yayin da Henry Ajumogobia ya ki amsa gayyatar. Tsagerun Neja-Deltan suna ta fasa bututun mai a yankin, kuma sun sha alwashin sai sun durkufar da tatar mai a yankin.

Kungiyar MEND na Neja-Delta ta saka mutane da za su shiga tattanawa da gwamnati ganin an tsaida wannan aika-aika da ya jefa tattalin arzikin kasar cikin wani hali. Wadanda aka saka sun hada da Ajumogobia SAN (Jihar Ribas); Bismark Rewane (Jihar Delta); Sanata Florence Ita-Giwa (Jihar Kuros-Riba); Timipa Jenkins Okponipere (Jihar Bayelsa); Ibanga Isine (Jihar Akwa Ibom); Ledum Mitee (Jihar Ribas); da kuma Lawson Omokhodion (Jihar Edo).

Sai dai Ajumogobia, wanda tsohon ministan mai ne na kasar, ya ki amsa goron gayyatar, a wata sanarwa da yayi. Na samu labarin ana ta yada cewa na amince in tattauna da gwamnatin tarayya game da fashe-fashen bututun mai da ake ta yi a Neja-Delta da yawun bakin wadannan mutane, to hakan ba gaskiya ba ne.

“Ina so in sanar da mutane cewa ban san wadannan mutane ba, kuma ba zan tattauna a matsayin su ba da gwamnatin tarayya. Wani da yake dan ikirarin kungiyar MEND ne ya kira ni a wayar tarho, ya tambayane ni ko ina da niyyar in shiga tattaunawar lumana da gwamnati wajen gano an samu kwacinyar hankali a yankin na Neja-Delta.“

Ministan man kasar, Ibe Kachikwu ya bayyana cewa Gwamnatin Muhammmadu Buhari za ta shiga tattaunawa da tsagerun na NDA, wanda suka dauki nauyin kai hare-hare da dama a yankin na Neja-Delta. Amma sai dai kungiyar ta ce ba za ta tattaunan ba, ta kuma kai hari kan bututun mai na kamfanin Chevron. Hare-haren dai ya kawo karancin hakar man da ake yi a wajen. A daidai wannan lokacin ne kuma wata kungiyar Joint Niger Delta Liberation Force ta sanar da tsagaita wuta da kuma sabon shirin yarejejeniyar tattaunawa.

 

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel