‘Yar shekara 45 ta haifi ‘yan ukku
Wata mace ‘yar shekara 45 a jihar Benue ta haifi ‘yan ukku bayan shekaru 12 ta na neman haihuwa
Shafin Pulse.ng ne ya rawaito cewa wani mai amfani da dandalin sada zumunta da muharawa na facebook ne ba da labarin hahuwar mai ban mamaki, bayan da matar 'yar shekara 45, ta zama abin batanci da yi wa zambo a wurin mijinta da kuma danginsa kan rashin haihuwa.
Matar 'yar shekara 45, a cewar su, ta haihu ne a Asibitin First Lady Hospital da ke garin Makurdi a ranar Litinin 13 ga watan Yuni, wanda hakan ya ba kowa mamaki musamman ma’aikatan asibitin da kuma mijin matar da kuma danginsa, bayan da tun farko asibitin da sun yanke cewa matar ‘yar asalin Oturko ba ta taba haihuwa ba. Labarin ya kara da cewa matar ta dauki ciki ne taikamakon wani tsari na kimiyya, ta haihu ne ta hanyar aikin da aka yi mata a inda aka cire jira-jiran.
A wani labarin kuma, wata ta haihu a bayan shekaru 25 ta na neman haihuwar, a cewara Adebukola Akinbabalola wani mai amfani da dandalin sada zumunta da muhawara, ya kara da cewa matar kawar wacce ta haifi ‘yan ukun ce, ta kuma yi addu’a ta neman wacce duk ba ta haihu ba, Allah Ya ba ta.
Asali: Legit.ng