An kama masu neman aikin yan'sanda biyar
-An kama maza biyar a lokacin daukar ma'aikatan yan'sanda a jihar Nasarawa, Lafiya
-An tsare mutanan ne a kan zargin bayar da takardar shaida na jabu da sata
Yan'sanda na jihar Nasarawa, sun kama masu neman aiki biyar, da tuhuma, kan amfani da takardar shaida na jabu da sata, a lokacin daukan Ma'aikatan yan'sanda a jihar Lafiya, a ranar Laraba. An rahoto cewa, hudu daga cikin masu neman aikin, sun bayar da takardan shaida na jabu, domin samun aiki a ma'aikatan yan'sanda, yayinda aka kama cikon na biyar din, da laifin satar wayar salula.
KU KARANTA KUMA: Olayinka na zargin makirci kan chajin shi
Alhassan Mamoda, kwamishinan yan'sanda da ke lura da daukan ma'aikata a jihar, yayi sharhi akan wadanda aka tsare: "Ka kwatanta, tayaya wanda ke neman shiga cikin ma'aikatan yan'sanda, domin kare rayuka, da kaddarorin mutane zai yi sata a gurin da a ke gudanar da tantance ma'aikata.
Ya sace wayar salular, ya kuma boye a cikin wandon sa, an gano shi, an kuma kama shi a lokacin da ake gudanar da bincike. An mika dukkansu a hannun jami'an da ya kamata, domin ci gaba da gudanar da bincike.
A cewar kwamishinan yan'sandan, an tantance musu neman aiki, 5,200 daga cikin mutane 9,627, da suke neman aiki a ma'aikatar, na yan'sandan jihar Nasarawa .
Asali: Legit.ng