Yan Boko Haram sun kashe masunta 42
- ‘Yan Boko Haram sun kashe masunta 42, an cire gawawwaki daga Tafkin Chadi.
–Sojoji sun sanar da cewa an tsinci gawawwakin masunta 42 da ‘Yan kungiyar ta’adda na Boko Haram suka kashe.
–An ciro gawawwakin su daga Tafkin Cad a Kamaru.
–An mika gawawwakin ga dangin su domin a bizne su.
‘Yan ta’addan Boko Haram sun hallaka mutane 42 a Darak. Kafin wannan harin, ‘Yan ta’addan sun kashe wasu masuntan 10 a wani gari mai makwabtaka na Touboun Ali a ranar Litinin 6 ga watan nan. Haka kuma ranar Jumu’a 3 ga watan Yunin dai sum kashe sojoji guda 32 a garin Bosso.
Kwanel Nomo Jean Claude ya sanar da majiya labarai na Afrika mai suna ‘Daily Sabah’ ta yanar gizo cewa mutanen kauyukan na Kamaru sun ga gawawwakin mutane a saman ruwa, sai suka sanar da jami’an tsaro nan take.
“Mun samu gawawwaki 42 a ruwa daga ranar Asabar zuwa Lahadi. Da muka bincika mu ka gane ‘Yan kasar Kamaru ne, da kuma Najeriya da Cadi. Tuni aka mika ma dangin su domin su rufe su.
A Safiyar ranar Talata ma ‘Yan Boko Haram din sun shiga garin Kautuva, inda suka kona gidaje da dama, su ka harbe wasu mutanen ‘yan kauyen, wanda hakan yayi sanadiyar mutuwar wasun su.
Mai magana da yawun bakin sojin Najeriya, Kwanel Sani Kukasheka Usman ya sanar ma manema labarai cewa wasu ‘yan kungiyar Boko Haram sun shiga kauyen Kutuva a babur inda suka kashe mutane 4, kuma suka sace mata guda 4 daga kauyen.
“’Yan bangan kauyen sun yi kokarin taka masu burki, amma abin bai ci tura ba, yayin da ‘Yan ta’addan suka tsere daji.”
“Sai dai ‘Yan bangan sun kwato wata yarinya ‘yar shekara 11, wanda tace an sato ne daga Kauyen Batha. Sai dai ba su samu kama ‘yan ta’addan ba ko kwato matan da suka sace”
Shekara 7 kenan ana fafatawa da ‘yan Boko Haram, fadan da yayi sanadiyar mutuwar mutane 20,000 har lahira da kuma mutane kimanin miliyan 2.7 da aka tarwatsar daga gidajen su. Fiye da mutane kuma 50,000 ne suka bar gidajen su a Kudu maso gabashin kasar a cewar gidan labarai na Fox News.
Nijar, Cadi, Benin da Kmaru sun hada rundunar gwigwa domin yakar wadannan ‘Yan ta’adda. Boko Haram din dai sun kona makarantu, masallatai da tashoshin mota, har ma da sace yara mata fiye da 200 daga Chibok suka sa su cikin bauta.
A Maris din 2016 ne wani kotu a kasar Kamaru ya yankewa ‘yan kungiyar su 89 hukuncin kisa. Hakan ya jawo ce-ce-ku-ce daga bankin masana harkar ta’addaci.
Asali: Legit.ng