Farashi a Najeriya ya haw-hawa da 15.6%
Kamar dai yadda wani rahoto da hukumar kididdiga da lissafi ta kasa watau National Bureau of Statistics ta fitar ya nuna cewa ma'aunin haw-hawar farashin kayayyaki ya tashi sosai sakamakon cire tallafin da gwamnatin tarayya tayi daga harkar man fetur wanda yayi sanadiyyar tashin farashin sa daga N87 zuwa N145 a duk lita daya.
Hukumar dai ta ce haw-hawar farashin da aka samu cikin watan Mayun da ya gabata ya nuna cewar kusan komai ya tashi a kasuwannin kasar idan aka kamata shi da watan Aprilu. Rahoton ya cigaba da cewa wannan baya rasa nasaba da karin kudin man fetur din da aka samu.
A cewar rahoton, a cikin watan Mayun da ya gabata dai alkaluma sun nuna karin cewar farashin kayayyaki ya kara tashi a karo na hudu a jere kenan kawo yanzu. Wani dalilin karin haw-hawan farashin kuma shine samun karin kudin wuta da akayi wanda shima akwai alaka mai karfi.
Rahoton ya cigaba da cewa cikin watannin nan kuma an samu karin farashin sufuri da tafiye-tafiye tun daga kudaden mota zuwa na fetur da saura kayan mota kamar bakin mai da ma kalazir. Tashin farashin kayayyakin da ake shigowa dasu kuwa ya koma 18.6% a watan Mayun nan daga 16.3% a watan Afrilu duk na 2016.
Wannan haw-hawar farashin dai na 15.6% shine mafi tsanani cikin yan shekarun nan tun bayan na 15.86% cikin watan Satumbar shekarar 2008. A wani labarin kuma mai kama da wannan, yan Najeriya zasu shiga wani kunci sakamakon kudirin da babbab bankin Nijeriya (CBN) ke shirin yi na kayyade iya kudin da yan Najeriya za su iya fiddawa daga asusun ajiyar su daga N10,000 sakamakon rashin kudi.
Asali: Legit.ng