wani mutun ya cutar da yan'mata hudu bayan ya ba su N50
-Rahoto ya nuna cewa mutumin da ake zargi ya yi nufin rage wa yan'matan hanya ne kafin ya aikata abunda ake zargin shi na cutar wa
-Rahotanni sun nuna cewa, iyayen yaran sun tabbatar da kai harin bayan sun kai yaran asibiti
A yanzu haka, Habibu Yaguda, na fuskantan caji akan, zargin cutar da yan'mata hudu a jihar Kano.
Nigerian Tribune, ya rahoto cewa, wani babban kotu a jihar Kano, ta yanke wa wanda a ke zargi, hukuncin zaman gidan kaso, bayan gwaji akan cutarwa. Yaguda ya kasance mazaunin kauyen Kofar Fada, a kusa da jihar Kano, amma ya ce bai aikata laifin da ake zargin shi ba. Hajiya Maryam Sabo, wacce ke shugabantan al'amarin, ta daga sauraron karan zuwa, 19 ga watan Yuni, bayan ta sa an tsare wanda ake kara a kurkuku.
KU KARANTA KUMA: rashin tsaro: Kiristocin Arewa sun koka
A cewar me bincike, mutane 3, Yusuf Musa, Abdullahi Yahaya da Yahuza Sale, sun rahoto al'amarin, a gidan yan sanda, na yankin Gezawa, a jihar.
Inspecta Musa, ya bayyana cewa, Yaguda ya ba yaran masu shekara 11 da 12 abin hannu, ya kuma bata su.
Yaci gaba da cewa, dan sandan ya lura da cewa, wanda ake kara, ya rage wa yaran hanya a motar sa, ya kuma dauke su zuwa gidan sa da ke kauyen Kofar Fada, inda ya ba ko wani dayansu N50. An tattara cewa lokacin da aka dauki yaran zuwa asibitin Gezawa General Hospital, likitoci sun tabbatar da kazantar, an kama wanda ake zargi da keta doka ta sashi 283 na shari'a.
Asali: Legit.ng