Balatoli yayi fada a gidan rawa a lokacin hutunsa
-An yi fada da Mario Balatoli a wani gidan rawa a bakin teku a Brescia, Italy
-Dan wasan na Italy ya koma Liverpool bayan da an ba da aronsa ga AC Milan
-Dan wasan gaban bai ji ciwo ba yayin da wani mutum ya rasa yantsunsa guda 3
-‘yan sanda na shirin kiran dan wasan don jin bayanin abin da ya faru.
Dan wasan gaba Mario Balatolli ya sa kansa a rigima bayan da ta tabbata cewa an yi wani fada da shi a kofar wani gidan a Italy. Ta kuma tabbata cewa a yayin fadar wani mutum ya rasa ‘yan yatsunsa guda uku a wani bakin teku da ke Brescia.
Fadan ya faru ne a dalilin wasu kalamai da aka ce an yi kan dan wasan wanda suka harzuka dan uwansa Enoch. Wata jaridar Italy mai suna daily Corriere della Seta ta rawaito cewa ba a san wanda ya ta da hatsaniyar ba, kuma za’a iya cewa ga irin rawar da dan kwallon ya taka a fadar ba.
LURA: Za ku iya samun labarai da dumi-duminsu a manhajjar Legit.ng sport
Wasu sun ce an ga dan wasa Balatolli na daukar hoto da wasu samari, wasu kuma sun ce da su a ka soma fadan, wanda daga baya Balatollin ya shiga.
Dan wasan dai yana hutu ne a wurin shakatawa na Brescia kwanaki kafin tsohon kulop din sa ya bayar da sanarwar cewa ba za su rike shi a kakar wasannin da za’a shiga ba, ana sa rai Balatollin zai yi atisaye da Liverpool kafin kakar wasannin idan ba’a sayar da shi ba kafin nan.
Asali: Legit.ng