Dasuki ya shigo da muggan makamai cikin kasa - Gwamnati

Dasuki ya shigo da muggan makamai cikin kasa - Gwamnati

- Kanal Sambo Dasuki (mai ritaya), tsohon mai bada shawara akan tsaron kasa (NSA) ga tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan da aka zarga da sayo muggan makamai zuwa cikin kasar

- Wannan tuhuma da  gwamnatin tarayya ta kawo a ranar Laraba, 8 ga Yuni, a wata Babbar Kotun Tarayya da ke zaune a Abuja, Babban  Birnin Tarayya

- Bisa ga gwamnati, manyan gungumen  makamai da harsasai Kanal Sambo Dasuki (mai ritaya) ya sayo.

Dasuki ya shigo da muggan makamai cikin kasa - Gwamnati
Sambo Dasuki

Gwamnatin tarayya taji tsõron cewa manyan muggan makamai na  hannun mutanen da suke goyon baya shi dasuki. Baya ga gwamnatin tarayya ta kai ƙara a kan tsohon mai bada shawara akan tsaron tsaron kasa, gwamanatin tarraya ta bukaci kotun ta ba da kariya ga masu shaidan da zasu bada shaida akan zargin cewa Dasuki ya mallaki makamai da harsasai ba bisa doka ba, kazalika da kudin haram.

Duk da haka, kotun ya farko ta ki yarda da yin hakan da aka yi,amma gwamnatin tarayya ta sake ƙaddamar da wani sabo a ranar Laraba, 8 ga Yuni, cewa ta ba da kariya ga masu bada shaida. Gwamnatin tarayya bata son  jama'a jama’a su san su.

A yayinda yake gabattar da rokon, lauyan gwamnatin tarayya, Oladipo Opeseyi ya nemi wani tsari don ba da damar da a kira shaidu da sunayen ƙarya, wanda ba ainihin sunayensu ba,a yayinda zasu bada shaida.

Dalilin da yasa gwamnati ta gabatakar da wannan  bukatar shine Dasuki, kasancewa sa tsohon NSA kuma babban tsohon jam’in soja mai ritaya, wanda a lokaci guda shi ne dan sarki a cibiyar daular usmaniiyya ta sakkwato,yana  da manyan mabiya a duk faɗin Najeriya, wanda zasu iya fusata a bisa ga shari'ar.

Gwamnatin tarayya ta kara da cewa, kulawa da rayuwan waɗanda yasu bada shaida na da muhimmanci,saboda rayukansu zai iya shiga miyagun hali  idan sun yi shaida a cikin jama'a ba tare da kariya ba, saboda haka, za’a bukaci yin amfani da sunayen karya.

A goyon bayan da aka ba wa bukatar  gwamnati da kuma a cikin wani rantsuwa sakin layi biyar da wani Emmanuel Ikpebe ya sallamar, gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa Dasuki yayi aiki a cikin bangaren naúra na soja ,  kuma cewa manya manyan makamai da harsasai da aka samu a gidansa , a lokacin da akayi bincike , bugu da kari,an samu kudaden  kasashen waje daban-daban wanda ya kasa bayanin inda ya samo su.

Yayinda yake ba da amsa , Joseph Daodu , lauyan dasuki , ya bukaci mai shari’a Adeniyi Ademola da ya bashi wasu lokaci dan ya bada amsoshi ga karar. Mai shari’ar Ademola ya bashi , bayan haka ,ya dakatar da kara zuwa Yuni 23 da 24 domin kara ji.

A gefe daya , tsofaffin ministoci guda biyu suna amsa tambayoyi a wurin  EFCC kan $ 115billion,kudin jama’an da tsohon ministan mai ,Diezani Alison - Madueke ta bayar dan yakin neman zaben 2015.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel