Abun tsoro:kofur ya aika abokin aikinsa lahira

Abun tsoro:kofur ya aika abokin aikinsa lahira

- Wani yan sanda, kofur ya kashe abokin aikinsa a kan dubu dari uku

- kofur Tosin wai harbe Shu'aibu bayan ya janye kudi har zuwa N300,000 a asirce daga asusun bankin Shu'aibu ba tare da sanin sa ba

Kamar yadda kaji, 'dan sanda kofur, Daramola Tosin, ya kashe wani jami'in' dan sanda, insfector Lateef Shu'aibu. A cewar wani rahoton ta jaridar Punch, Kofur Tosin Tuni dai aka sallame shi sannan aka tura shi offishin yan sanda na karamar hukumar ekiti,ta jihar kwara.

KU KARANTA: Wasu Gwamnonin Arewa sun gana da Oyegun a Imo

Tosin wai ya harbe Shu'aibu bayan ya janye kudi har zuwa N300,000 a asirce daga asusun bankin Shu'aibu ba tare da sanin sa ba . An tattara cewa Shu'aibu ya danƙa wa Tosin katin sarrafa kudin shi ne a lõkacin da ya fadi rashin lafiya.

An bayar da rahoton cewa Insfector din na ba haya ne a lõkacin Tosin ya harbe shi da wata bindigaAK-47 kuma ya binne shi a bayan barikin 'yan sanda . 'yar'uwar wanda aka kashe, Sherifat Hammed, ta kai kara offishin yan sanda a ranar goma ga watan mayu shekara dubu biyu da goma sha shida( May 10, 2016),cewa dan uwanta shuaibu fa ya bace tun shida da watar mayu.. Tace tana zargin Tosin saboda yayanta ya fadi mata cewan ya danƙa wa tosin katin sarrafa kudinsa ta bankin UBA dan ya tayashi ciro kudi.

Magana akan al'amarin, kwamishinan 'yan sanda na jihar Kwara, Sam Okaula, ya ce ya tabbatar da cewan an gudanar da bincike , ya kara da cewa an kama abun zargin. Kwamishanan ya ce, "Ba mu amince da aikata laifi ba . Muna kama kowani mamba na jami’an ‘yan sandan da yayi laifi. Za mu gudanar da bincike da kuma gurfanar da su. " An gurfanar da tosin ne a ranar Talata, 8 ga Yuni a kotun Majistare da ke garin Ilori.

majistaren, Mr. Nurudeen Adeyanju, wanda yaki daukan hujjan abun zargin, ya ce kotu n sa ba ta da ikon akan al'amarin tunda cajin kisa ne. Ya kara da cewa shi ya kamata a abar wa babbar kotu. Duk da haka da umarrnin cewa a kulle tosin a Kurkukun tarayya dake , Mandalla. An dakatar da karar zuna ranar 21 ga watan Yuni, 2016.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng