Jihar Sakkwato za ta samar da hekta 1000 na kiwo
- Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Tambuwal ya ce jihar za ta samar da fili hekta 1000 domin kiwo.- Tambuwal ya ce jihar a shirye ta ke ta samar da filaye na yin noma don
- riba ga duk wani dan kasuwa da ke shirin zuba jari a noman zamani
- Tambuwal ya kuma ce gwammnatin jihar za ta kaddamar da shirin samar da madara domin riba kafin karshen shekarar nan
Gwamnatin ta kuma ce a shirye ta ke da ta samar da filayen noma ga masu son zuba jari domin yin noma na zamani da injina domin riba a jihar.
A wata sanarwa da ofishin gwamnan ya fitar a Sakkwato, wanda kuma Malam Imam Imama ya sa hannu ta ce, Tambuwal ya yi wannan jawabi ne a yayin bikin bude wani taro a kan kiwo da kuma samar da madara wanda ma’aikatar kula da ayyukan gona da bunkasa karkara ta gudanar.
“Tsarin mai inganci na samar da kebabbun filayen kiwo zai inganta lafiyar shanun mu. Ta hakan kuma za mu iya sa ido a kan abinda dabbobi suke ci, mu kuma kiyasta irin abubuwan da zamu amfana daga jikinsu”.
Tunanina shi ne makiyaya na yin kaura ne daga wannan wuri zuwa wancan don nema wurin kiwo mai ni’ima, amma idan za mu iya samar da irin wadannan wurare a kusa da su, na yi amanna za su zauna wuri guda. Sakkwato za ta tallafawa duk wani yunkuri na inganta kiwon dabbobi da kuma samar da madara” a cewar gwamnan.
“Muna nan muna aiki da abokan huldarmu a Argentina, na tabbatar da yiwuwar wannan shiri. Burin mu shi ne mu soma aiki gadan-gadan domin ganin an soma cin gajiyar shirin. Muna da aniyar soma aiki a watan Oktobar wannan shekara kuma muna fatan hakan zai taimakawa yawan adadin madarar da ake samarwa a kasar nan. Wannan shiri ne mai muhimmanci saboda zai samar da ayyukan yi ga ‘yan kasa, za kuma su kara ilimin yadda ake noman zaman”. A cewar Tambuwal din.
A wani labarin kuma, gwamnan jihar Ogun Olusegun Mimiko ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta amince da kafa kebbabun wurare na kiwo ba a jiharsa. Mimiko ya jaddada cewa shirin kirkiro da kebabbun wuraren kiwo ba ya cikin kundin tsarin mulkin kasar na 1999 wanda aka yi wa gyaran-fuska.
Asali: Legit.ng