An Kama Wani Shugaban Tsagerun Nija Delta a Bayelsa

An Kama Wani Shugaban Tsagerun Nija Delta a Bayelsa

Jami'an tsaron Najeriya na Civil Defence watau -Nigerian Security and Civil Defence Corps (NSCDC)- sun bayyana cewar sun kama wani babban shugaban tsagerun Naija-delta.

An Kama Wani Shugaban Tsagerun Nija Delta a Bayelsa

Masu fasa bututun wadan da suka fasa bututun da bi ta Tabidaba zuwa Brass har Azuzuama zuwa Ikienghenbiri dake cikin karamar hukumar Ijaw ta Kudu a jihar Bayelsa. Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa wanda aka kama din sunan sa Suoyo Nathan kuma an kama shine a jiya litinin tare da taimakon wasu jami'an tsaron masu yawon sintiri.

A cewar rundunar kuma yanzu haka suna neman wasu tsagerun masu suna Iyalewei da kuma Fyneboy. Rundunar kuma ta kara da cewa suna nan suna ta kokari domin bankado tare da gano masu fasa bututun mai a ko ina suke.

A wani labarin kuma, Gwamnatin Najeriya na shirin shiga sulhu da tsagerun Nija Delta Avengers domin samun zaman lafiya a yankin. Wannan yazo ne bayan da Gwamnatin ta bada umurni ga sojojin Najeriya dasu murkushe kungiyar yan ta'addan sannan kuma ta hana su fasa bututun da suke yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel