Sultan na Sokoto ya sanar da farkon Ramadan

Sultan na Sokoto ya sanar da farkon Ramadan

- Yan Najeriya su fara azumin Ramadan a ranar 6 ga watan Yuni kamar  yadda Sulta ya sanar da farawanta

- Ya kuma yi Allah wadai da fille kan mace a jihar Kano domin zargin sabo

Sultan na Sokoto, Muhammad Sa’ad Abubakar, ya sanar da farkon Ramadan a ranar Litinin, 6 ga watan Yuni, bayan ganin sabon wata a gurare daban daban.

Sultan yace anga wata a gurare da dama a dukan fadin Najeriya kuma kamar yadda irin wannan musulmai ke jiran a fara tsawon watan azumi kamar yadda kamar yadda Allah Madaukaki ya fada a cikin Alkur’ani mai girma

Sultan na Sokoto ya sanar da farkon Ramadan
Sultan na Sokoto mai suna Muhammadu Sa'ad Abubakar

Yace: “Ina da mafi girma da yardarsa zuwa ga bushara a gare ku cewa a yau biyar ga watan Yuni, 2016 ya nuna alaman karshen watan Shaaban sabili da haka shida ga watan Yuni, shekara ta 2016 ne farkon Ramadan 1437 AH.

“Rahoto abin dogaro daga shuwagabannin musulmai a fadin kasa ya nuna cewa anga sabon watan Ramandan a gurare daban-daban na kasar. Ina rokon ku dukka da kuyi amfani da wannan damar gurin addu’a akan zaman lafiya da kuma ci gaban wannan kasar.”

Abubakar ya shawarci dukkan muslmai akan suyi amfani da wannan lokaci suyi addu’a akan ci gaban mulkin Najeriya da kuma zaman lafiya. Sultan yaci gaba da shawartan su akan ci gaba da jitu dangantaka da juna ba tare da la’akari da addini da kabilanci da kuma bambance-bambace ba.

A cikin irin ci gaba, ya yi Allah wadai da kashe-kashen yan kiristoci a jihar Kano da jihar Niger akan kammata sabo. Ya bayyana kisan da rashin tausayi da kuma rashin koyi da musulunci, ya kuma yi kira ga yan Najeriya da su guji ayyuka da zai haifar da warwarewar doka da tsarin shari’a.

A lokaci guda, shugaba Muhammadu Buhari ya ce watan Ramadan ya kasance lokaci na farfado da ruhaniya ba barin abinci da ruwan sha ba kawai, amma kuma daga dukkan savo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel