Najeriya ce kasa ta 4 wajen karfin soji a Afirika - Rahoto

Najeriya ce kasa ta 4 wajen karfin soji a Afirika - Rahoto

- Najeriya ce kas ta 4 wajen karfin soji a Nahiyar Afirika

- Misira, Algeria da  Habasha da ne kasashe 3 na farko

- Kungiyar Global Fire Power ce ta gudanar da binciken

 

Najeriya ce kasa ta 4 wajen karfin soji a Afirika - Rahoto
Sojojin Najeriya a cigaba da yaki da Boko Haram a yankin arewa maso Gabashin Najeriya
Asali: Facebook

Sojin Najeriya ne na 4 mafi karfi a Nahiyar Afirika. Wannan yazo ne daga kungiyar Global Fire Power inda ta bayyana cewa Misira, Algeria da Habasha ne 3 na farko.

Kungiyar tayib jerin kasashe 30 na farko masu karfin soji inda ta sanya Afirika ta Kudu bayan Najeriya. Kungiyar ta bayyana cewa ta duba yawan sojoji, makaman zamani, albarkatun mai wajen tantance manyan 30 na farko doin da wadannan ne ake yin yaki a wannan zamanin.

Kungiyar ta bayyana cewa tana duba yawan makamn da kasa take dasu iri-iri, makamin kare dangi da kuma kungiyoyin hadin gwiwa irin su NATO a cikin tantancewar.

A cigaban jerin bayan Afirika ta Kudu wadda tazo ta 5 bayan Najeriya, akwai  Angola, Morocco, Sudan, Libya, Democratic Republic of Congo, Kenya, Tunisia, Zimbabwe, Zambia, Chad, Uganda, Tanzania, South Sudan and Ghana.

Sauran kasashen kuma sune; Cameroon, Mozambique, Niger, Ivory Coast, Mali, Madagascar, Gabon, Republic of the Congo, Namibia, Somalia and Central African Republic.

Wannan na zuwa ne bayan da sojojin Najeriya suka ceci daya daga cikin Yan Matan Chibok, Amina Ali Nkek da Boko Haram ta sace su 219 daga makarantarSakandare ta Yan Mata dake a garin Chibok, Jihar Borno.

A duniya gaba daya, kasar Amurka ce ta 1, sai kasar Rasha ta 2, sai kasar Indiya sannan kasar Ingila. Amurka ta jima tana zama ta 1 tun 1945 take rike da wannan lamba a duniya ma baki daya.

A wani labarin kuma, hukumar sojin Najeriya ta bayyana cewa wani dan Boko Haram ya kashe shugaban masu kera ma kungiyar Bam da wasu manyan kwamandojin kungiyar. Hukumar sojin ta bayyana cewa  ta samu labarin ne daga wata yar kunar bakin wake data kama wadda tayi kokarin tada Bam a kasuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng