Ajandar yaki da rashawa guda 7 na shugaba Buhari

Ajandar yaki da rashawa guda 7 na shugaba Buhari

– Shugaban kasa Buhari ya fitar da sabbin matakai a kokarin sa na kara kaimi wajen yaki da cin hanci da rashawa a Nigeria

– Shugaban ya bukaci a inganta gaskiya a bangaren tattalin arziki kasa da kuma yaki da cin hanci a sashen kasuwancin man fetur

Ajandar yaki da rashawa guda 7 na shugaba Buhari
Shugaba Buhari

A shirye shiryen sa na ziyarar UK, shugaban kasa Buhari ya fitar da matakan kara kaimi wajen yaki dacin hanci da rashawa. An saki matakan ne ajiya a Abuja daga hannun mai taimakawa shugaban wajen yada labarai, wato Mallam Garba Shehu.

KU KARANTA: adakalar kudi: Minista na fuskantar tuhuma daga Buhari

Matakan dai sun hada da:

1. Habaka gaskiya a bangarorin tattalin arziki da kuma tilasta bin dokokin yaki da almundahana a bangaren kasuwancin man fetur na kasa

2. Kwarara dokokin da suka shafi yaki da cin hanci da rashawa

3. Saka matakan yaki da cin hanci da rashawa a bangaren shugabancin kamfanoni na kasa

4. Shigar da dokar taimakekeniya tsakanin kasa da kasa wajen kama masu laifi ta shekara 2016

5. Hana wadanda suka yi babakere da kudaden kasa fita da kuma saka jarin kudaden satar a kasashen waje

6. Fito da sunayen wadanda ake tuhuma da almundahana da kuma wadanda aka riga aka yanke ma hukunci da kuma rarraba sunayen ga gwamnatocin kaseshen waje

7. Buga Kwangilolin da suka kai wani mataki tare da sunayen masu kamfanonin da suke karawa wajen samun su domin kowa ya gani

Asali: Legit.ng

Online view pixel