Manyan labarai guda 10 wadanda sukayi fice a ranar Juma'a

Manyan labarai guda 10 wadanda sukayi fice a ranar Juma'a

Legit.ng ta tattara maku manyan labarai guda 10 wadanda sukayi fice a ranar Juma'a 6 ga watan Mayu na 2016. Ku duba domin ku samu manyan labaran.

Manyan labarai guda 10 wadanda sukayi fice a ranar Juma'a

1. Makarantun Sakandare na Abuja na cikin mafi kyau a Najeriya

Hukumar WAEC ta saki wani jerin sunaye wanda ke nuna cewa makarantun Abuja suna cikin kyau a Najeriya.

KU KARANTA: An kama wani matashi saboda rubutu a Facebook

2. Obasanjo tagwaye ne?

Wani amfani da Facebook, Akpodhoma Mike Ajirioghene Mikoko ya saki wasu hotuna wadanda ke nun amani mai kama da tsohon shugaban kasar Najeriya, Obasanjo

3. Shugaban kasa Buhari ya sanya ma kasafin kudi hannu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya ma kasafin kudi na 2016 hannu a jiya.

4. Ana cigaba da kokawa akan kisan da Fulani sukayi ma mutane a Enugu

Ana cigaba da kokawa a Uwo-Uwanni yadda Fulani suka kaima mutane hari a can

5. Abunda Buhari ya fada bayan sanya ma kasafin kudi hannu

Legit.ng ta tattara abubuwa guda 12 wadanda shugaban kasa Buhari ya bayyana bayan daya sanya ma kasafin kudi hannu.

6. Lai Muhammad ya bayyana cewa an murkushe Boko Haram

Ministan labarai, Lai Muhammad ya bayyana cewa an murkushe yan kungiyar Boko Haram.

7. Abubuwan dake sa mutum ya kasa haihuwa

A lokaci da yawa ana ganin laifin iyaye mata idan ma'aurata suka kasa haihuwa. Ba a koda yaushe bane laifin su.

8. Kotu ta yanke ma matar aure da saurayin ta hukuncin kisa

Bayan an gano cewa su suka kashe mijin  matar kuma su lalata gawar shi, kotun Ebonyi ta yanke masu hukuncin kisa.

9. Hukumar EFCC ta gayyaci Femi Fani Kayode

Hukumar Efcc ta gayyaci tsohon Ministan Jiragen sama, kumjmai'i mai hudda da jama'a na kungiyar yakin neman zaben tsohon shugaban kasa Jonathan.

10. Subhnallahi" Wani mutum ya kai ubangiji kara Kotu

A kasar Isira'ila ne wani mutum mai suna  David Shoshan ya kai karar Ubangiji kotun kasar

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng