Manyan labarai 10 da sukayi fice a ranar Alhamis

Manyan labarai 10 da sukayi fice a ranar Alhamis

Legit.ng ta tattara maku manyan labarai guda 10 wadanda sukayi fice a ranar Alhmis 5a gawatan Mayu. Ku duba domin ku samu manyan labaran.

Manyan labarai 10 da sukayi fice a ranar Alhamis
Shugaba Buhari da shugaban UNODC

1. Yan Boko Haram sun farma sojojin Najeriya a Sambisa

Sojojin Najeriya sun samu kansu a kan harin yan kungiyar Boko Haram bayan da sukayi shiga dajin Sambisa neman yan Ta'addan. Wannan ya faru ne a jiya Alhamis 5 ga watan Mayu na 2016.

KU KARANTA: Buhari: Majalisar Dinkin Duniya ta maido mana da kudaden mu da wuri

2. Tsagerun Nija Delta sun fasa Bututun Mai

tsagerun Nija Delta sun fasa wani Bututun Mai a Warri dake a jihar Delta. Tsagerun kuma sun bada gargadi a gwamnatin Najeriya inda sukayi barazanar kai hari a Abuja da Legas.

3.  Shugaban Buhari ya gana da kungiyar G-19 ta APC a Abuja

Shugaba muhammadu Buhari ya gana da yn kungiyar G-19 a fadar shugaban kasa dake a babban Birnin Tarayya, Abuja.

4. Gwamnatin Tarayya ta bayyana manyan aiyuka da shugaban kasa ke son yi guda 34

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa akwai manya manyan aiyuka guda 34 da shugaban kasa Muhammadu Buhari yake son aiwatarwa a kasafin kudi na 2016.

5. Sojoji sun tare wani hari daga Makiyaya a jihar Zamfara

Sojojin Najeriya sunyi nasarar tare wani hari da makiyaya suka nemi su kai a Jihar Zamfara.

6. Abunda ya sanya na saki wasikar Sanusi Lamido

Ministan Sufuri Rotimi Ameachi, ya bayyana dalilan daya sanya ya saki wasikar da Sanusi Lamido ya rubuta ma Jonathan akan baccewar Dala Biliyan 49.

7. Ana rikici a Aba

Ana rikici a Aba dake a Jihar Abia inda Igbo da Hausawa ke fada.

8. Shugaba Buhari zaya sanya hannu a kasafin kudi a ranar Juma'a

A yau ne ake tsammanin shugaban kasa Muhammadu Buhari zaya sanya hannu akan kasafin kudi na 2016.

9.  Matar Tinubu ta samu nadin mukami

Shugaban majalisa, Bukola Saraki, ya nada Sanata Remi Tinubu a matsayin mukaddashin mai tsawatarwa na majalisar Dattawan najeriya.

10. Hptuna daga harin da Fulani suka kai a Enugu

A cigaba da jimami da akyi a Enugu, wasu hotuna sun fito masu ban tausai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel