Ya dawo da kafar dama: Ronaldo ya zura biyu yayinda Manchester ta narki Newcastle 4:1

Ya dawo da kafar dama: Ronaldo ya zura biyu yayinda Manchester ta narki Newcastle 4:1

  • Daga dawowarsa, Cristiano Ronaldo ya cigaba daga inda ya tsaye na tozarta gololin Firimiya
  • A wasarsa ta farko, Ronaldo ya taya Manchestr nasara kan Newcastle United

Cristiano Ronaldo ya dawo Manchester United bayan shekaru 12 da kafar dama yayinda ya zura kwallaye biyu a nasarar da United ta samu kan Newcastle ranar Asabar.

Manchester United ta lallasa Newcastle 4:1 a filin wasansu ta Old Trafford.

Yanzu dai Ronaldo na da jimillar kwallaye 120 a wasar Firimiya.

Ronaldo ya zura kwallon farko ne a minti 45 + 2 ana gab da zuwa hutun rabin lokaci, kafin J. Manquillo na Newcastle ya rama a daidai minti na 56.

Bayan minti 8 da Newcastle ta rama, Ronaldo ya sake zura kwallonsa ta biyu a minti na 62.

Kara karanta wannan

Sanatocin Najeriya sun garzaya Landan don gaishe da Tinubu

Manchester ta fara shakar kamshin nasara kenan Bruno Fernandes ya ci wata kwallo maikyau daga nesa a minti na 80.

Yayinda ake gab da shi a minti na 92, Jesse Lingard, ya zura kwallo ta hudu bayan tsawon lokaci bai takawa Manchester leda ba.

Kalli hotunan wasan:

Ya dawo da kafar dama: Ronaldo ya zura biyu yayinda Manchester ta narki Newcastle 4:1
Ya dawo da kafar dama: Ronaldo ya zura biyu yayinda Manchester ta narki Newcastle 4:1
Asali: Getty Images

Asali: Facebook

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng